Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Kungiyar shugabannin makarantun Sakandire ta Kasa sun gudanar da taron horo ga ‘yan kungiyar na shiyyar Arewa maso yamma da jihar Kano ta dauki bakunci da aka gudanar a babban dakin taro na Coronation a gidan Gwamnatin Kano.
Taron ya sami halartar ‘yan kungiyar da suka fito daga jihohi Bakwai na Arewa maso yamma da kuma shugaban kungiyar na kasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Da yake zantawa da :yan jarida, shugaban kungiyar shugabannin makarantun Sakandire na kasa Muhammad Bin Musa ya ce suna taron ne don karawa shugabannin makarantun ilimi, domin kullum abubuwa na tasowa sauyi domin su san abin da yake da yanda zai gudanar da harkar sa a makaranta ba kawai ya je ya zauna a ofis yana kula da malamai bane da dalibai yana kula ne da duk abubuwa dake gudana a makarantar da kula da harkar tsaro ma.
Ya ce don su ake wannan irin taro na yiwa kansu bita don kara ilimi da kuma inganta ayyukan su a makarantu duk lokacin da suka yi irin wannan taruka shugabannin suka koma makarantun su tara malamai su nuna musu abin da aka yi don a hudu ayi aiki da su.
Ya yi nuni da cewa ba zai yiwu shugaban makaranta ya yi aikin shi kadai ba, dole sai an hadu da sauran malamai akwai mataimakan su in sun koma za su fadakar da su abin da suka koya saboda a gudu tare a tsira tare don samar da inganci a kula da tafiyar da makarantu.
Shugaban na kasa Malam Muhammad bin Musa ya ce suna jan hankalin masu ruwa da tsaki su sani duk lokacin da shugabannin makarantun Sakandire za su yi irin wannan taro su sani ba taro ne na sharholiya ba, taro ne na karin ilimi duk abin da suka koya za su je suyi amfani dashi ne don inganta ilimi ne.
Kuma Kungiyar tasu ba kawai a Nijeriya kadai ake da ita ba, ta Duniya ce suna halartar taruka a kasashen Duniya ko shugaban su na Afirka da ya gama dan Nijeriya ne.
Muhammad Bin Musa ya roki gwamnatoci na jihohi kasar nan musamman duk lokacin da za a yi irin wadannan taro su rika taimakawa kungiyarar shugabannin makarantun Sakandire domin su sami halarta don ba karamin ilimi suke samu ba saboda ba kowace jiha ce take wa malamai bita irin wannan.ba a taron ne suke samun damar da suke dashi na bibiyar abubuwa da suke damun su dan samun mafita..
Da take zantawa da ‘yan jarida mai masaukin baki taron shugabar kungiyar shugabannin makarantun Sakandire ta jihar Kano, Shugabar GGSS ‘Yar Gaya Hajiya Uwani Ahmad Balarabe ta ce makasudin taron shi ne duk shekara ana haduwa ayi taron a shiyyoyi hudu, wannan na Arewa maso yamma ne ana zabar jihar da zata karbi bakuncin jihohi Bakwai a taru ayi bita ta sanin makamar kwarewa da zasu tafiyar da shugabancin makarantunsu.
Ta ce wannan da ake a Kano shi ne cika makon wanda aka yi a dukkan shiyyoyin kasar nan wanda shi ne na karshe a bana sai badi kuma duk dai domin tattauna abubuwa da suka dame su da hanyoyi da za a bi don magance su saboda a sami ci gaban ilimi.
Hajiya Uwani Ahmad Balarabe ta yabawa Gwamnatin jihar Kano bisa irin cikakkiyar gudunmuwa da suka basu domin gudanar da taron kuma ita uwar kungiyar tasu ta kawo taron na bana jihar Kano ne ganin yadda ya zama shi ne gwarzo a harkar ilmi duk ƙasar nan har ya sami lambar yabo wannan ya sa kungiyar su suka zabi Kano don yin taron domin su zo ganewa idonsu irin ci gaba da aka samu.






