Wed. May 14th, 2025

Karrama Kwankwaso: An Ajiye Ƙwarya A Gurbinta Ne -Hon Nura Dala

By Saleh Aliyu May 11, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Babban hadimi na musamman ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Hon. Nura Mai Ƙarfi Dala, ya bayyana karramawar da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil, Kano ta yi wa Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da digirin girmamawa da cewa an ajiye ƙwarya a gurbinta ne.

Ya ce ba Kwankwaso digirin girmamawar tabbas an yi abin da ya kamata, musamman idan aka yi la’akari da irin gudummuwa da ya bai wa jihar kano a ɓangaren ilimi.

Hon. Nura Me Ƙarfi Dala, ya yi nuni da cewa su ma waɗanda Jami’ar ta karrama da suka haɗa da shugaban kamfanin AMASCO, Alhaji Mustapha Ado da Alhaji Ɗahiru Barau Mangal da Alhaji Aliko Ɗangote a matsayin iyayen Jami’ar, mutane ne da Allah ya horewa arziƙi suke yin hidima ga al’umma. Ya roƙi Allah ya yawaita irin su, sannan kuma ‘yan baya da suke tasowa su yi koyi da su wajen ba da gudunmuwa ga cigaban al’umma.

Ita ma Hajiya Rahana Iliyasu mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano shawara kan harkokin mata ta ce, duk ɗaukakar da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ke samu daga Allah ne, saboda irin kishinsa da son cigaban a’umma, musamman talakawa. “Don haka yake ta samun ɗaukaka a rayuwarsa”, in ji ta.

Da yake zantawa da manema labara, Alhaji Shehu Tijjani mai kula da ofishin Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga ya ce, waɗanda aka karrama tun daga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Aliko Ɗangote, Alhaji Mustapha AMMASCO da Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, suna ba da mutuƙar gudunmuwa wajen tallafawa cigaban ilimi.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *