Daga Ibrahim Muhammad
Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta jihar Kano ke yi domin kawo ƙarshen ayyukan rashin ɗa’a da ke yawaita a kafafen sada zumunta na zamani, ta samu nasarar kama wasu matasa guda huɗu masu amfani da manhajar TikTok da ake zargi da nuna rashin tarbiyya da kalamai marasa ma’ana inda aka gurfanar da su gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman, jami’in yaɗa labarai na Hukumar ya raba wa manema labarai.
Tun da farko a zaman kotun bayan mai gabatar da ƙara Batista Garzali Maigari Bichi ya karantowa waɗanda ake zargi, Hafsa Hamisu (Zoom-Zoom), Usman Majidaɗi (Majidaɗi) Sumayya Muhammad (Summy Beby) da Usman Ibrahim (Maikalar Kuɗi), tuhume-tuhumen da ake musu dukkanninsu nan take suka amsa.
Sai dai Mai Shari’a Halima Wali ta kotun Noman Sland, ta ɗage sauraran ƙarar daga 28/5/2025 zuwa 2/6/2025, tare da ba da umarnin a ajiye su a gidan gyaran hali har ranar da za a dawo domin yanke masu hukunci.
Ko a watanin da suka gabata, Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jahar Kano, ta aike da irin wadannan matasa gaban kotu domin ladabtar da su, inda kotun bayan samun su da laifi ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya ko zaɓin biyan tara N100,000 da wanda za su karɓe su da bisa sharaɗin irin haka ba za ta ƙara faruwa ba.
Wannan dai wani yunƙuri ne da Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano ke yi domin kawo gyara, tare da daƙile irin rashin tarbiyyar da wasu matasa ke nunawa a kafafen sada zumunta a jihar Kano, wanda yin hakan ya ci karo da tsarin al’ada ta zamantakewa, tare da koyarwar addinin Musulunci.






