Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Hukuncin Babbar Kotun Tarayya a Kan Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta rushe hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke a kan zaɓen kananan hukumomi a jihar, inda ta bayyana cewa kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraron shari’ar da ta shafi batun gudanar da zaɓen.

Premier Radio ta rawaito cewa tun da farko, jam’iyyar APC tare da wasu mutane ne suka shigar da ƙara gaban babbar kotun tarayya domin neman dakatar da zaɓen, bisa zargin cewa shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano na da alaka da jam’iyyar NNPP, wadda ke mulkin jihar.

Sai dai a hukuncin da mai shari’a Oyewumi ya karanta, ya bayyana cewa kotun tarayyar ta ƙetare iyakar huruminta wajen sauraron ƙarar, balle har ta yanke hukunci a kai. Bisa haka, kotun ɗaukaka ƙara ta amince da ƙorafin da gwamnatin jihar Kano ta gabatar, tare da soke hukuncin babbar kotun.

Wannan hukunci na nufin zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar zai ci gaba da kasancewa halastacce a idon doka, inda kuma shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin su za su ci gaba da zama akan kujerun su na mulki.

Mun ciro daga shafin Daily Nigerian

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe