Da cikakken alhini da juyayi, kungiyar ‘Kannywood Film Industry Guilds and Associations (KAFIGAN)’ na mika ta’aziyyarta ga al’ummar Jihar Kano baki daya, bisa rasuwar Alhaji Abbas Muhammadu Sanusi, Galadiman Kano kuma babban jigo a masarautar Kano.
Marigayi Galadiman Kano, wanda ya rasu yana da shekaru 92 bayan jinya mai tsawo, ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jJihar Kano.
Shugaban kwamitin Amintattu na KAFIGAN, Alhaji Isma’il Na’Abba (Afakallah), ya bayyana marigayin a matsayin ginshiki mai mahimmanci a tsarin masarautun gargajiya, wanda gudunmawarsa wajen ci gaban masarautu da adana al’adu za su kasance abin tunawa ba ma a Jihar Kano kadai ba, a kasar da ma duniya baki daya.
Isma’il Na’Abba Afakallah ya mika ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kano, majalisar masarautar Kano, da iyalan marigayin, tare da yin addu’a Allah Ya gafarta ma sa kuma Ya sa Jannatul Firdausi makoma a gare shi.
Sa hannu:
Al-Amin Ciroma
Daraktan Yada Labarai da Harkokin Jama’a.






