Daga Ibrahim Muhammad
Abin farin ciki ne mu taya ya’yanmu murna bisa karatu da suka yi har wasu suka fita da sakamako kyakkyawar a wannan jam’ia ta Aliko Ɗangote da jagora sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya kafa .
Alhaji Abdulkadir Gambo Ɗankoli ne ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida a yayin karrama Kwankwaso da jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil ta yi ya ce suna alfahari da wannan katafaren taro da tun kafuwar jami’ar baya jin an taba taro da mashahuran mutane masu mulki da sarauta da attajirai suka taru don bikin yaye wadannan dalibai da karrama mutane.
Yace wannan abin jin dadi ne Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso shi ya samar da wannan jami’a ta kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote saboda kishin talaka da dan talaka.
Alhaji Abdulkadir Gambo Dankoli ya ce suna farin ciki da jin dadi da karramawa da jami’ar ta yiwa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso duba da gudummawa da ya bayar na kafa jami’ar ta habaka.
Ya ce da Kwankwaso bai yi tunanin samar da Jami’ar Wudil ba da wannan alherin ba za a same shi ba suna godewa sauran wadanda suke bada gudunmawa wajen haɓakar jami’ar.
Ya kara da cewa Allah ya sakawa jagora tsohon Gwamna, tsohon minista tsohon dan takarar shugabancin kasar nan na NNPP Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da alkhari ,wannan gudummawa da ya assasa dama sun sani shi jagora ne kuma jirgi ne wajen gudanar da cigaban ilimi a jihar Kano da Nijeriya gaba daya.
Alhaji Abdukadir Gambo Dankoli ya yi kira ga magoya baya da masu tasowa idan suka sami dama suyi koyi da jagoran Kwankwasiyya yanda ya zo ya kafa jami’o’i guda biyu a jihar Kano bayan makarantu na gaba da Sakandare 24 da ya samar da kuma tura dalibai ya’yan talakawa karatu waje da mafi yawa sun gama suna anfanar da cigaban al’umma.








