Daga Ibrahim Muhammad
An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar ‘yan Tifa na ƙasa reshen jihar Kano wanda a yayin taron tsohon shugaban ƙungiyar da ya yi wa’adi biyu da ya kawo mata ɗimbin cigaba.
Hon. Mamunu Ibrahim Takai ya ja hankalin ‘yan ƙungiyar a kan yin aiki tuƙuru don ƙara bunƙasa cigabata.
Ya bayyana taron na rantsar da sabbin shugabannin ‘yan Tifa na jihar Kano da suka fito a mabambantan kujeru na takara tun daga kan shugaba har mukamai na ƙasa da aka yi zaɓe na masallaha da fahimtar juna bisa yardar duk ‘yan ƙungiyar aka tabbatar da ƙunshin sabon shugabanci.
Ya ce sun gode wa Allah da mutum huɗu da suka yi takarar neman shugabancin ƙungiyar Yahuza Umar da Ɗan Asabe da Ibrahim Shafi’i Zainawa da Isah Ja’afar Ƙofar Na’isa dukkanin su yanzu na cikin ƙunshin shugabanci da Kwamared Isah Ja’afar ya sami kansa a matsayin shugaba.
Hon. Mamunu Ibrahim Takai ya ja hankalin sabbin shugabannin da cewa su sani su shugabanni da suka gabata har zuwa kansu suna gode wa Allah domin sun auri Tifa sun yi zama da ita saboda Allah ta sami ciki kuma yau ta haife su, don haka su sani cewa salin alim suka fito kamar yadda da yake fitowa daga cikin mahaifiyarsa, don haka su mayar da hankali irin ƙoƙarin da suka yi a baya na shugabanci su yi abin da ya fi nasu.
Hon. Mamunu Ibrahim Takai da a lokacin shugabancin su na ƙungiyar ‘yan Tifa na jihar Kano sun gina mata sakatariya na dindindin sun kuma inganta alaka tsakaninsu da gwamnati da ɓangarori na jami’an tsaro shi ya sa ma ya ce aka ga fuskokin su a tare da su a taron.
Ya yi nuni da cewa tun daga lokacin da aka yi zaɓe na farko a ƙungiyar ‘yan Tifa na jihar Kano a shekarar 2017 aka zaɓe shi a matsayin shugaba ya shekara huɗu a kai aka sake yin zaɓe a 2021 aka sake zaɓensa a karo na biyu a matsayin shugaba ya shekara uku da ‘yan kwanaki ya sauka ya bai wa mataimakinsa ya ƙarasa shekara ɗaya.
Ya gode wa Allah bisa irin ɗimbin nasarori da suka samu a cikin shekara takwas daga mafi muhimmancin nasara da suka samu shi ne na haɗa kan ‘yan ƙungiyar da gudanar da shirya tarukan ƙarawa juna sani ga mambobinsu da haɗin gwiwa da ofishin VIO na jihar Kano da Hukumar Road Safety da KAROTA. Wannan ta sa aka sami gyara a harkokin Tifa sosai, in aka yi waiwaye da tarihin ƙungiyar Tifa a baya kafin zuwansu an sami bambanci da shekaru takwas da suka yi, an sami cigaba da natsuwa da ƙarin kwanciyar hankali a cikin sana’arsu mai albarka.
Hon. Kwamared Mamunu Ibrahim Takai da a lokacin da yake shugabancin ƙungiyar sun yi mata riga da wando da hula da takalmi har ma da afa sun gode wa Allah da wannan dama da ya ba su ba da alfahari ba sun sami ƙungiya ba ta da komai sun yi mata tsari sun gina ta tana samun cigaba.






