Samar Da Tiransifoma A Mazaɓar Gwagwarwa, Usman Miloniya ya yaba wa ɗan Majalisar Tarayya na Nasarawa, Hassan Shehu Husain

Daga Ibrahim Muhammad

Al’ummar mazaɓar Gwagwarwa da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ba za su manta da irin mutuntasu da ɗan Majalisarsu na Tarayyar mai wakiltar ƙaramar hukumar, Hon. Hassan Shehu Hussain ya yi ba na samar musu da tiransifoma a mazaɓar.

Jigo a jam’iyyar APC Muƙaddashin shugaban ƙungiyar APC ƙadangare bakin tulu na jihar Kano, Alhaji Usman Miloniya Gwagwarwa ne ya bayyana hakan ga jaridar AMANAPRESS a Kano.

Ya ce a baya lokacin da suke da mataimakin Gwamnan Kano ɗan mazaɓar Gawuna Nasiru Yusuf Gawuna a gwamnatin Ganduje ba irin koken da ba su kai masa ba a kan ya sama musu tiransifomar har ma bayan shi sun riƙa godo a wajen wasu jagorari na APC, amma har aka kayar da su a mulki ba su iya samar musu ba.

Usman Miloniya ya ce rashin tiransifomar a Gwagwarwa ya jefa mutane a mawuyacin hali na rashin samun wuta ya kassara ƙananan sana’o’i da mata da matasa suke yi a gidaje da unguwanni sun shiga halin matsi da kaka na ka yi har sai wannan lokaci da ɗan Majalisar Nasarawa ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.’, Hon. Hassan Shehu Husain ya samar musu wannan abin jin daɗi ne ga al’ummar Gwagwarwa.

Ya ƙara da cewa wani abin jin daɗi da nuna sanin yakamata da nuna damuwa da ɗan Majalisar Nasarawa ya yi musu shi ne tare shi ma al’ummar Gwagwarwa suka yi a kan hanya suka koka masa a kan buƙatar samar musu da tiransifomar, kuma cikin ikon Allah ga shi ya samar musu, abin da gwamnatinsu ta APC da ta wuce ta kasa yi musu.

Alhaji Usman Miloniya Gwagwarwa ya yi fatan ɗan Majalisar Nasarawa, Hon.Hasaan Shehu Hussain zai zai ɗore a irin wannan hali nasa na sauraren jama’a da kuma biya musu buƙatunsu da yin ayyuka da suke gani yana aiwatarwa na hanyoyi da tallafa wa al’umma.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo