Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana ɗimbin jama’a da suka zo ɗaurin auren na gidan mai bai wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf shawara na musamman a kan harkokin siyasa, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso da cewa ya nuna irin kyakkyawar mu’amala da tsari da yake ga dukkan al’umma, shi ya sa mutane suke tare da shi a dukkan sha’aninsu.
Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Ambasada Hon. Isyaku Yahaya Talba ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Kwankwaso.
Ya yi fatan Ango da Amarya Allah ya zaunar da su lafiya da yin haƙuri da juna, Allah ya sa albarka a auren, ya kawo alheri da zuriyya nagari ɗayyaba.
Ya ƙara da cewa yadda al’umma ta taru don shaida auren ya nuna duk jihar Kano ba wata jam’iyya bayan ta NNPP, kuma babu wani Jagora da ya wuce Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sun gode wa Allah da ya zama tsarin Kwankwasiyya yana haifa da alkhairi mai yawa a tsakanin jama’a.
Talba ya ƙara da cewa irin ayyuka da mai girma Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yake na kulawa da cigaban al’umma birni da karkara, mutane suna gamsuwa da tsarin gwamnatinsa da tsarin Kwankwasiyya.
Ambassada Isyaku Yahaya Talba ya ce, suna fata a zaɓen 2027 Jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama shugaban ƙasar Nijeriya gaba ɗaya domin zai kai ta ga tudun-mun-tsira.







