Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa mafi yawan manyan masu riƙe da muƙamai a Gwamnatin Tarayya da zaɓaɓɓu ‘yan jam’iyyar APC daga jihar Kano sune kan gaba wajen ƙiyayya da irin muhimman ayyukan cigaban da Gwamnatin NNPP take kawowa alhali mafi yawan al’ummar jihar Kano na gamsuwa da sam-barka ne ayyukanda take.
Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Ambasada Isyaku Yahaya Talba ne ya bayyana haka a martani da ya mayar ga Sanatan jam’iyyar APC na Kano ta Arewa, Barau I Jibrin kan kalamai da ya yi na rashin adalci cewa Kano tana samun koma-baya.
Ya yi nuni da cewa tsabar hassadace da son rai da makauniyar adawa da irin rashin jin daɗi na irin ɗimbin ayyukan raya ƙasa da na cigaban al’umma da gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP take yi mutuƙar ɓata musu rai da tayar musu da hankali da tona asirin irin ɓarnar da gwamnatinsu da ta gabata ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta yi shi ya sa suke maganganu na ɗimaucewa.
Ya ƙara da cewa hakan tasa kullum ba su da wani ƙulle-ƙulle sai na yin sharri da neman ganin gazawar gwamnanatin Kano, amma sun kasa kullum gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsarin Kwankwasiyya sai cigaba take wajen gudanar da ayyuka a ko’ina a faɗin Kano.
Ambasada Isyaku Yahaya Talba ya ƙara da cewa a bayyane take ga al’ummar jihar Kano da suka fito ƙwai da ƙwarƙwata suka zaɓi wannan gwamnati ta Injiniya Abba Kabir Yusuf domin tun a zaɓen shekara ta 2019 suka zaɓe shi, amma aka yi musu kwacen zaɓin su don haka a 2023 suka sake tabbatar da zaɓen Abba Kabir Yusuf don tsira daga danniya da wawashe musu dukiya da ake yi a baya.
Ya ƙara da cewa tun zuwan gwamnatin Abba Kabir Yusuf wasu maƙiya cigaban Kano daga jam’iyyar adawa ta APC ke ta ɓullo da makirce-makirci don haifar da matsaloli domin su kawar da hankalin Gwamnan Kano ga barin yi wa al’umma aiki.
Sun kai shi ƙara kotu don a k’ƙwace zaɓen ba su yi nasara ba, suka yi ta ƙoƙarin haddasa rigimar masarauta da rura fitinar ‘yan daba a unguwanni, amma hakan bai kawar da hankalin gwamnatin Kano daga yi wa al’ummarta ayyuka ba da ƙoƙarin inganta tsaro.
Ambassada Isyaku Yahaya Talba ya ce mutanen jihar Kano masu karamci ne da sanin ya kamata, suna zaune lafiya da bai wa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf haɗin kai da goyon baya, suna kuma gamsuwa da irin ayyuka da yake, a gefe daya kuma suna lura da makiyansu da ƙoƙarin haifar da koma-baya da rashin zaman lafiya da suke ƙullawa, kuma ba za su taɓa samun nasara kan mummunar manufarsu ba da yardar Allah.
Ya ce al’ummar jihar Kano mutane ne masu mutuntaka da ƙaunar juna da sanin ‘yancin kansu babu wani da zai zo da kuɗi ya rufe musu ido, suna kallon kima ne da mutunci da aiki tuƙuru da riƙon amana da ake musu a tsarin Kwankwasiyya.
Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Ambasada Isyaku Yahaya Talba ya ce al’ummar jihar Kano suna tare da gwamnatin Abba Kabir Yusuf, suna gamsuwa da aikin da yake musu ba tare da nuna bambanci ba. Hatta ‘yan jam’iyyar adawa ana ba su haƙƙinsu ana biyan tsofaffin kansilolin APC haƙƙinsu.
Ambasada Isyaku Yahaya Talba ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su cigaba da bai wa gwamnatin Injiniya Abbas Kabir Yusuf goyon baya da taya jihar Kano addu’a na cigaba da samun zaman lafiya da cigaba da yi mata addu’a ta neman kariya daga maƙiyanta na gida da na waje.






