Masu Haɗa Magunguna Suna Da Daraja A Cikin Al’umma -Stephen Daniel

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana masu haɗa magunguna a cikin al’umma da zama gagara-misali, saboda irin gudunmawar da suke bayarwa.

Sakatarem dindindin a Ma’aikatar Raya Dabbobi da Lafiyarsu na jihar Filato, Mista Stephen D. Daniel ne ya bayyana hakan a Kano a taron ƙasa na harhada magunguna.

Ya ba da misali na cewa a matsayinsa na Kirista, Littafi Mai Tsarki ya nuna musu Allah ya bai wa Isa Almasihu damar wakar da kowace irin cuta, “Amma idan ka karanta Littafin da kyau za ka ga akwai makaho da ya sami Almasihu duk da yana da iko da zai ce idon ya buɗe, amma bai faɗi haka ba.”

Ya ci gaba da cewa, “Sai ya sami magani ya sa masa a idon ya ce ya je ya wanke, sai da wanke sannan ya samu gani. Wannan ya nuna maganar magani ya yana da muhimmanci. Don haka masu haɗa magunguna na masu daraja da bai kamata a yi wasa da su ba.”

Mista Stephen ya ƙara da nuna cewa wani shugaban ƙasa da aka taɓa yi a ƙasar Amurka da ya ce idan ba ka da mai haɗa magunguna ka samu. Sannan yana kuma tausayawa mutane da ba su san muhimmancin masu haɗa magunguna ba.

Ya koka da cewa yanzu cikin matsalolin da ake da su a cikin magungunan da muke sha, sune kuma suke haifar mana da cuta saboda mutane ba sa zuwa su sami masana magunguna suna gaya masa wanda ya dace, domin ba kowane magani ne za ka sha ba in kana rashin lafiya. “Shi ma maganin na da nasa cutarwar in ba a sha yadda ya dace ba,” ya jadadda.

Da yake magana a kan kiwon dabbobi ya ce, “A baya iyaye da kakanni sun daraja kiwon dabbobi sosai, amma yanzu an zo wani lokaci da ko saboda an yi karatun zamani ne? Sai aka kauce daga hanyar kiwo, amma shugaban ƙasa Ahmad Bola Tinubu yana so ya dawo da ‘yan ƙasar nan kan hanya na kiwo,” in ji shi.

Mista Stephen Daniel ya ce, shugaba Tinubu ya ƙirƙiri Ma’aikatar Kula Kiwo Dabbobi ne don bai wa kowa dama ya yi kiwo na zamani wanda hakan zai kawo ƙarshen irin rikice-rikicen da ake samu tsakanin manoma da makiyaya. “Yanzu a jihar Filato akwai irin wannan Ma’aikata da Gwamnan Filato ya samar ana aiki sosai domin kyautata kiwon dabbobi,” ya ƙarƙare.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe