Daga Ibrahim Muhammad
An gudanar da bikin rabaon tallafi jari da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayar ga mata guda 200 a ƙaramar hukumar Fagge daga mazaɓu 10 na yanki a ranar Littafin.
Taron rabon tallafin da aka gudanar a harabar sakatariyar ƙaramar hukumar Fagge ya sami halartar mai bai wa Gwamnan Kano shawara na musamman a kan cigaban ƙungiyoyi, Hon. Nasir Garba Kunya wanda ya wakilci Gwmnan.
Da yake jawabi a taron, shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Salisu Usman Masu ya bayyana cewa rabon tallafin na daga cika alƙawari da Gwamnan jihar Kano ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe na cigaba da tsari da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso karo na ɗaya da na biyu ta yi na tallafa wa mata da matasa da jari.
Ya ce wannan ba shi ne tallafi na farko ba, an yi sau da dama, kuma a wannan karon an tallafa wa mata 200 ne kowacce da ₦50,000. “Don haka jama’a su cigaba da yi wa Gwamna addu’a da yi masa fata na alkhari,” in ji shi.
Shugaban ƙaramar hukumar Fagge ya yi nuni da cewa a jihar Kano bai taɓa ganin wani lokaci da ya ga ana ayyuka na raya ƙasa irin wannan lokaci na Gwamna Abba Kabir Yusuf ba, “In za a tuna titunan garin nan sun lalace, amma a yanzu ɗaiɗaiku ne wanda ba a ƙararsa gyara su ba. Ana gudanar da ayyuka daban-daban da suka shafi cigaban al’umma,” ya jadadda.
Ya ja hankalin mata da suka amfana da tallafin jarin da cewa ₦50,000 da aka bai wa kowace mace nata ne ɗari bisa ɗari kar wasu su ce ta ba su, amma ba a hana ta yi alheri ko da ga mijinta ba bane na ‘yar ₦500 ya ɗan taɓa.
Ya yi fatan waɗanda suka amfana da jarin su yi amfani da shi ta ƙirƙirowa kansu sana’a da za su riƙa yi don dogaro da kai.
Hon. Salisu Masu ya sake jaddada kira da roƙo ga mata da suka amfana su je su yi wani abu da za su dogara da kai ta yadda jarin zai riƙa sama musu abin da za su riƙa samun wani abu a sana’o’i da za su yi.
Tunda farko Wakilin Gwamnan jihar Kano a taron rabon tallafin mai bai wa Gwamna shawara a kan cigaban ƙungiyoyi, Hon. Nasiru Garba Kunya ya bayyana cewa dukkanin abubuwan da Gwamna ya yi alƙawari yana ƙoƙarin ya cika, kuma a tsarin Kwankwasiyya tunda ake tafiya sama da shekara 20 jagoransu Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yana siyasa da tsari, yana taimaka wa al’ummar jihar Kano da suke fatan taimakon zai isa ga waɗansu nan gaba daya.
Ya ce Gwamna ya yi alƙawarin tallafa wa mata da matasa. “Saboda haka tun kafa wannan gwamnati duk da wasu marasa kishin Kano sun yi ta haifar da matsaloli domin su kawo wa Kano tarnaƙi, amma Allah bai ɗauke hankalin Gwamna ba wajen cika alƙawari da ya yi yana kan cikawa,” in ji shi.
Ya ce Gwamna a ƙarƙashin Hukumar CRC yana bai wa mata na ƙananan hukumomim Kano kuɗaɗe domin tallafa wa mata da jari kusan karo na biyar ke nan da ake tallafa wa mata a ƙananan hukumomi 44 da ke Kano.
Ya yi jan hankalin mata da cewa kamar yadda Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cika alƙawarinsa su ma su ɗauki alƙawari na bai wa Gwamna goyon baya ya ɗora cigaban mulkinsa kuma waɗanda suka amfana su yi amfani da jarin don yin ƙananan sana’o’i, dama kuma suna alfahari da ƙaramar hukumar Fagge don dama mata da matasansu da ‘yan mata da yara ƙanana sun goge wajen yin ƙananan sana’o’i.
Ya kafa misali da cewa kasuwanni da ake da su da suke kusa da Fagge akwai ƙananan sana’o’i da yawanci mata da suke Fagge ne suke yi.
Ya jijina wa al’ummar Fagge da suka ɗauki yin sana’o’i da muhimmanci, kuma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ɗauki raba jari da muhimmanci.
A jawabinsa, shugaban Kwamitin CRC na ƙaramar hukumar Fagge, Alhaji Habu Muhammad da Sakataren Kwamitin Alhaji Jazuli Abdullahi ya wakilta ya ce, maƙasudin taron rabon tallafin cigaba da cika alƙawari da Gwamna ya yi ne a lokacin yaƙin neman zaɓe na tallafa wa mata da matasa da jari domin yin sana’o’in da za su taimaka wa kansu da iyalansu.






