Daga Ibrahim Muhammad
Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano Muhammad Naziru Ya’u na tsawon wata uku.
Majalisar dokokin ta ɗauki matakin ne saboda rahotanni da ake samu na zargin yin almundahana da kuma rashin tañuka wani abun a zo a gani.
Ana zargin shugaban ƙaramar hukumar Hon. Naziru da sayar da takin zamani da jihar Kano ta ba shi domin ya sayarwa manoman a farashi mai sauƙi.







