Al’ummar Mazaɓar Fagge C, Kano Sun Nuna Gamsuwa Da Ayyukan Hon. Sunusi Shariff

Daga Ibrahim Muhammad

Kansila mai wakiltar mazaɓar Fagge C a jihar Kano, Hon. Sanusi Shariff Kantoma ya gudanar da muhimman ayyuka a ƙoƙarin kyautata cigaban al’ummar mazaɓarsa.

Kamar yadda jaridar AMANA PRESS ta tabbatar, daga cikin ayyukan da Kansilan ya gudanar a ƙasa a halin yanzu sun haɗa da gina banɗakuna guda biyu a Tsangayar Malam Lawan a lungun Baban Kara domin amfanar almajiran da ke karatu a Tsangayar. Ya yi gyara na mayar da makewayin da ke ‘Yan Babura na zamani da ƙawata shi da tayils.

Sannan a ɓangaren kyautata yanayin samar da ilimi da kyautata muhalli mai kyau, Hon. Kantoma ya yi wa makarantar Islamiyya ta Dini Wal Tarbiyya da masallacin Malam Garba kwaskwarima gaba ɗaya.

Sannan ya yi rumfa ta masu gyara a ‘Yan Babura, tare da yin wata sabuwar rumfar a layin S. Laure.

Ayyukan da Kansilan na mazaɓar na Fagge C a yankin ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Sanusi Shariff Kantoma ya gudanar na daga cikin tsarin ayyuka da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Gwamna injiniya Abba Kabir Yusuf ta sahale wa Kansiloli su aiwatar a 2025.

Masu gudanar da harkokin gyara da saye da sayarwa a ‘Yan Babura a Mazaɓar Fagge C, sun bayyana mutuƙar jin daɗi da farin ciki bisa rumfa da gyaran banɗakin da Kansilan ya yi.

Mutane da dama sun bayyana cewa gina sabbin ban ɗakuna guda biyu da Kansila Sunusi Shariff Kantoma ya yi a Tsangayar Malam Lawan da cewa ya yi sara a kan gaɓa, kuma sun yi farin ciki da aikin. Don hakan mataki ne na kyautata tsafta a Tsangayar da gidajen maƙwabta a lungun da samawa almajirai sauƙi na magewayi.

Jigo a jam’iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Habu Ibrahim da sauran masu ruwa da tsaki na mazaɓar a kewayen ziyarar gani da ido na duba ayyukan da Kansilan Fagge C, Hon. Sanusi Shariff ya yi, sun bayyana gamsuwa da irin ƙoƙarinsa na yin ayyukan masu nagarta da za su amfani al’umma.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength