Daga Ibrahim Muhammad
Mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Isah Umaru ya yi kira ga ‘yan asalin ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a kan su cigaba da haɗa kansu da tafiya tare domin bunƙasa cigaban al’ummar yankin.
Ya bayyana haka ne a yayin taron karrama ‘yan asalin Rano da ke ayyuka daban-daban a faɗin ƙasar nan da aka yi a garin Rano ranar Asabar.
Ya kuma ja hankalin mutanen da aka karrama su buɗe wata ƙungiya ta daban su haɗa kai da ƙungiyar RAKIBU da za su riƙa fito da al’amuran da zai taimaka ga cigaban al’ummar masarautar Rano.
Mai martaba Sarkin na Rano Alhaji Muhammad Isah Umaru ya bayyana mutuƙar jin daɗinsa da farin ciki da Allah ya azurta su da mutane masu kishi da kima da daraja da suke kula da cigaban yankin da kuma ɗaukaka kimar ta a duniya ya yi fatan duk mutumin yankin da ya sami kansa a ko’ina zai zama jakada nagari ga yankin da kuma ba da kulawa ga cigaban al’umma.
Da yake zantawa da ‘yan jarida a kan maƙasudin taron Umar Yunusa Rano da aka fi sani da Ɗanburan shugaban gamayyar ƙungiyar cigaban Rano, Kibiya, Bunkure da aka fi sani da RAKIBU Rano, Kibiya, Bunkure development Association, ya ce, an samar da ƙungiyar ne tun a baya sakamakon raba ƙananan hukumomi da aka yi bayan suna dunƙule a waje ɗaya sai suka fahimci abin kamar zai kawo rabuwar kai alhali suna tare iyaye da kakanni komai tare suke yi.
Don haka suka ga cigaba ba zai samu ba a daidai ku sai an haɗu wannan ya sa suka haɗu aka samar da ƙungiyar ta RAKIBU a shekarar 2009, kuma an sanar da cigaba masu tarin yawa daga kafa ta ta wannan alakar an jajirce wajen taimakawa samar da hanyoyi wadatattu masu inganci da suka taso daga Ƙarfi har zuwa garin Sumaila da Bebeji. Sannan an samar da tsayayyen wutar lantarki da samar da asibitoci da makarantu daban-daban da kyakkyawan mu’amala da dukkan shugabannin da suke yankin ana yin magana da murya ɗaya a faɗa a ji.
Ya ce wannan taro na karramawa an yi shi ne don iya mutane da suka fito daga Rano da suka sami cigaba a fannoni daban-daban, amma an haɗu a Rano, Kibiya, Bunkure an gabatar gaba ɗaya, kuma a ciki ‘yan kowace jam’iyya sun zo an yi taro an haɗu an yi shawarwari ba wani da ya sa bambancin siyasa.
Ya ce a cikin waɗanda aka karrama ba a kalli wani yana siyasa kaza ba an duba cancanta da daidaito ne da irin gudunmawar da suka bayar na cigaban yanki da ake buƙata, sun yi ƙoƙarin kaucewa siyasa ta kowace siga a tsara taron karramawar.
Shugaban na RAKIBU ya ce an karrama mutane 19 ne, kuma a cikinsu akwai Farfesoshi guda bakwai da shugaban gidan Radiyo na jihar Kano Adamu Abubakar Rano, wanda shi ne na farko da suka taɓa samu daga yankin ya sami muƙamin. Sun karrama wacce ta soma samun Kwamishina ta farko daga mata a yankin Hajiya A’isha Lawan Saje da kuma manyan daraktoci a hukumomin gwamnati na tarayya da manyan ‘yan sanda, kuma wannan sun soma ne da kaso na farko, nan gaba za a zaɓi wasu a karrama su.
Ya ƙara da cewa bayan haka kamar yadda aka yi a Rano za kuma su je Kibiya irin waɗannan mutane da suke da su za su fito da su su yi a can.
Haka kuma za a yi a Bunkure saboda gaba ɗaya. Wannan shi yake nuna ana tare a dunƙule komai da komai tare ake yi gaba ɗaya.
Umar Yunusa Rano Danburan ya ce cigaba baya zuwa wajen mutane in suna zaune sai ita al’umma ta jajirce ta mike ta tashi tsaye ta je ta nemo abin da zai kawo musu cigaba ita kuma ɓangare gwamnati in aka yi duba da uzururruka na yi mata yawa, za ta ce za ta yi aiki kaza da kaza, amma abubuwa da suke tasowa yau da kullum sai a ga aikin ma sai a manta da shi ba a zo an yi a kan lokaci ba, sai a ce sai a tara sai wata shekarar, amma idan akwai jajircewar al’umma suna bibiya yau da gobe in Allah ya yarda za ta taimaka wa sanarwa shugabanni abin da al’umma ke buƙata.
Cikin mutane da aka karrama sun haɗa da Alhaji AA Rano da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya Hon. Alhasan Rurum da sauran mutane da suka haɗa da jami’an tsaro da ‘yan kasuwa da sauran masu muƙamai a ɓangarori da dama ‘yan yankin.






