Daga Ibrahim Muhammad
Ambasada Dakta Bashir Yusuf Abdullahi, mataimakin shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar Kwanar Singa da aka fi sani da SIMDA, ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu Allah ya kawo sauƙi na farashin kayan masarufi yana raguwa duba da duk shekara akwai yanayi ake samu, “Wannan shekara Allah ya kawo sauƙi tun daga yanzu a kan kayan yau da kullum na al’umma” in ji shi.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce, “Mu kanmu ‘yan kasuwa muna kuka da cewa kaya ba sa sayuwa, sai ma faɗuwa da muke yi saboda tsada. Sannan wani lokacin ma irin wannan na gabatowar Azumin watan Ramadan, sai a ga kaya suna ta tashi, kuma ba domin son ‘yan kasuwar ba, yanayi ne, amma a wannan karo duk wanda ka tambaya a kasuwa da daɗi, babu daɗi zai gaya maka farashin kaya na sauka ba kamar a baya ba,” in ji shi.
Ambasada Bashir Abdullahi ya ce fatan da suke da yardar Allah nan da cikin watan Azumi kayayyaki za su ci gaba da sauka al’umma su sami sauƙin yin Azumi a gama lafiya.
Ya yi kira ga ‘yan kasuwa manya da ƙanana a kan kowa ya ji tsoron Allah, “Idan aka ce kaya ya sauka, ka samo cikin rangwame, ya kamata ka yi duba a kan abin da ka sayo da yadda za ka sayar domin Allah na ya ganin ka. Idan ka bar shi a tsada ba ka san lokacin da asara za ta zo maka ba. Duk wata asara da za a ga ta zo akwai dalilinta. Wani ko da Allah ya ƙaddara ɗin za ka ga wani abu akwai sababi na wani ya yi wani abu yana ganin wayonsa ne ko dabararsa, sai Ubangiji ya nuna masa ta wani ɓangare. Amma idan akaji tsoron Allah aka duba aka tausaya, sai ka ga Allah ya tausaya, ko asarar ce ta zo sai ta zo mai sauƙi,” ya jaddada.
Ambasa Bashir Yusuf Abdullahi ya ce al’amarin harkar Dala da ake amfani da ita wajen kasuwanci abin ya taɓarɓare, daga sama ne duba da a shekarun baya za a ga farashin a ƙasa ne, amma yanzu za ka ji an yi kasafi a kan wani mataki na Dala duk iya ƙoƙarinka ba ka isa ka yi ƙasa da wannan matsayin na sama da aka yi ba dole sai dai ka yi shi a haka. “Alhakin gwamnati ne ta samar da daidaito a farashin Dala hakan zai taimaka,” ya jaddada.






