Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ɗaya daga cikin manajojin kamfanin Bukari Food Oil, Yusuf Muhammad Sulaiman da ake kira da Sahibi masu sarrafa man girki, ya nuna farin ciki da suka zama daga cikin waɗanda aka gayyata bukin ranar ingancin kaya ta duniya da Hukumar SON ta gudanar.
Ya ce kamfaninsu yana ba da kulawa wajen samar da kaya mai inganci, kuma shugaban kamfanin nasu mutum ne wanda yake dama tsayayye ne da ba da kulawa a kan duk wani abu da ya shafi harkokin kamfanin.
Yusuf Muhammad Sulaiman ya ƙara da cewa mallakin kamfanin na Bukari Food Oil na bayar da kyakkyawan kulawa da tabbatar da ana yin abin da ake sarrafawa mai inganci yana kula da kyautatawa ma’aikata, don haka duk masu ruwa da tsaki a aikin kamfanin suna yin tsayin daka don tabbatar da komai yana tafiya bisa inganci musamman da yake abin da suke samarwa mai ne na girki da ya shafi gina lafiyar al’umma.
Sahibi ya ce za su cigaba ba bin dokoki da ƙa’idodi da yin duk abin da ya dace domin bai wa Hukumar SON haɗin kai da goyon baya wajen ganin ana sanar da kayayyaki da suke da inganci a tsakanin al’umma.






