Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) reshen jihar Kano, ta kama matashin da ya soki jami’inta da makami a yunƙurinsu na tserewa da kayan mayen da suke ɗauke da shi.
Sadiq Muhammad Maigatari ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aika wa manema labarai a safiyar Laraba ya ce, lamarin ya faru ne a shatele-talen Rahama da ke ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano.
Ya ce sun kama natasan Musa Usman da Buhari Ya’u Bashir, a lokacin da suke ƙoƙarin shigowa da kayan mayen samfurin Tabar Wiwi Kilogram 1.1, Diazepam grams 8 (Fakiti 38), da kuma Exol grams 59 (Fakiti 165)”.
Ya ƙara da cewa, “A yayin da jami’anmu na Shiyyar Ƙiru suke ƙoƙarin kama su ne shi Musa Usman, ya ji wa jami’inmu mummunan rauni ta hanyar sukar sa da Ɗanbuda.”
Kwamandan hukumar na jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya yi Allah-wadai da wannan ɗanyen aiki da suka yi, har ma ya ba da tabbacin irin wannan ɗabi’a ta masu aikata laifin ba za ta sare musu gwiwa ba.
Sadiq Mai Gatari ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike a kan waɗanda ake zargin, kuma za su gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin su da aikata laifukan safarar kayan maye da kuma cin zarafin jami’in hukumar.






