Daga Ibrahim Muhammad
Kwamared Yahaya Yakub Umar Shugaban ƙungiyar ma’aikata sakatarori da masu aikin kwamfuta da masu ɗauko rahoto na ma’aikatan gwamnati na jihar Kano, ya cire wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf a kan yadda take kula da ma’aikata.
Kwamared Umar ya bayyana cewa, Ranar Ma’aikata, rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin tunawa da ma’aikata.
Ya ce a kasar nan a jihar Kano aka fara shi lokacin Gwamna Abubakar Rimi har ƙasar ta ɗauka gaba ɗaya. Don haka Kano ta fi kowa alfahari da farin ciki rana da za ma’aikata za su fito su bayyana matsaloli da buƙatunsu da kuma godiya ga shugabanni.
Shugaban ƙungiyar NUPSRAW ya bayyana gamsuwa da irin kulawar da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf take bai wa ma’aikata tun daga zuwanta ta zama abokiyar ma’aikata ta irin alkhairai da suke da yawa na kyautata masu da suka haɗa da biyan kuɗaɗen ma’aikata da suka yi ritaya garatuti da suke bi bashi da biyan karin kudin mafi ƙarancin albashi da aka zartar da wuri da kuma biyan albashi kafin ƙarshen wata ga ma’aikata da sauran abubuwa da dama.
Kwamared Yahaya Yakub Umar ya yi kira ga Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a kan ya cigaba da biyan kuɗaɗen garatuti da ya soma biya na sama da kashi 30, yanzu suna fata daga nan zuwa shekara ɗaya kamar yadda ya yi alƙawari Allah ya sa su ga ya gama biyan kuɗin gaba ɗaya.






