Sauƙaƙa Farashi Na Jawo Albarka A Kasuwanci -Alhaji Ibrahim Ɗanyaro

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban Dattawa na kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da Kasuwar Singa, Alhaji Ibrahim Ɗanyaro, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa yadda ake samun kayayyaki na masarufi da farashinsu ke raguwa a kullum.

Ya ce suna gode wa Allah da wannan ni’ima domin ita ce rahama da Allah ya kawo a cikin wannan al’umma a halin da ake ciki na tsananin rayuwa.

Ya yi nuni da cewa lokacin da kaya ba sa raguwa sai hauhawa suna tsada kullum za a yi ta kuka, yanzu kuma sauƙi yana zuwa don haka ya kamata a gode wa Allah.

Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya yi kira ga ‘yan kasuwa ƙanana da ke a unguwanni cikin saƙo da lunguna idan sun sai kaya da sauƙi su je su sayar da sauƙi domin abin da ya kamata ke nan shi ne albarkar kasuwanci.

Ya ce Manzon Allah (SAW) yana madalla da bawan da idan ya sayo da sauƙi zai sayar da sauƙi. “Saboda haka bai kamata su sai kaya da sauƙi ba, sannan su koma cikin al’umma su tsananta musu ba,” in ji shi.

Alhaji Ibrahim Ɗanyaro ya ja hankalin al’umma idan sun sami dama gwargwado su riƙa fitowa suna sayen kaya a inda suke gani ya fi sauƙi shi ne za ka san an sami rangwame.

Ɗanyaro ya jaddada kira ga ‘yan kasuwa idan sun sami kaya da sauƙi su sauƙaƙa wa jama’a, “Domin yanzu kullum kaya a kasuwa yana ƙasa ne, kuma muna fata da yardar Allah daga nan har Azumi kaya ƙasa za su yi ta yi,” ya jaddada.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe