Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Jagoran ‘yan’uwa Musulmi da aka fi sani Shi’a a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya halarci addu’ar bakwai ta rasuwar fitaccen malamin addini, Shaikh Ɗahiru Usman da aka yi jiya Alhamis a Bauchi.
An gudanar da taron ne a masallacin marigayin da ke unguwar Maƙera, inda ɗan’uwansa shaƙiƙi, Malam Badamasi Yaqoub, da ɗansa Muhammad Zakzaky suka wakilce shi.
Yayin isar da saƙon ta’aziyyar, Malam Badamasi ya ce rasuwar Sheikh Ɗahiru babban rashi ne ga al’ummar Musulmi.

Ya ce Sheikh Ɗahiru, wanda ya shahara da tafsirin Alƙur’ani ba tare da littafi a gabansa ba, ya taka gagarumar rawa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci a tsawon shekaru.
“Mahaddacin Alƙur’ani ne da babu kamarsa. Duk duniya ba a samu malamin da yake tafsiri da kai irin nasa ba,” inji shi.
Ya ce Sheikh Ɗahiru ya taimaki Musulmi ba tare da la’akari da ɓangaranci ko ƙabilanci ba, yana mai cewa:
“Ko kana tare da shi ko ba ka tare da shi, iliminsa ya amfane ka. Malaminka ne saboda hidimtar da ya yi wa addini.”

Ya ƙara da cewa saboda muhimmancin wannan rashi, Shaikh Zakzaky ya turo iyalai da ‘yan’uwansa domin su bayyana girmamawa da ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Malam Badamasi ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya kuma sanya kabarinsa ya zama rayuwa ta aljanna.
A jawabinsa na amsa ta’aziyyar, Khalifa Shaikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi ya gode wa Shaikh Zakzaky bisa zumuncin da ke tsakaninsu, yana mai cewa marigayin ya sha karɓar baƙuncinsa a lokutan baya.
“Shaikh Zakzaky ba baƙo ba ne a wannan gida. Sau da yawa idan ya zo, Shehi da kan sa yakan gabatar da shi ya jagoranci sallah,” in ji Khalifan.
Ya yi addu’ar Allah ya ɗaukaka Musulunci da Musulmi, ya kuma ƙara haɗa kan al’ummar Nijeriya.
Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu ne da safiyar Alhamis ɗin makon jiya, kuma jiya aka cika kwanaki bakwai da rasuwarsa.
Jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan suna ta ci gaba da zuwa gaisuwar ta’aziyya.






