Dubban ɗaruruwan al’ummar Musulmai za su hallara a yau Juma’a da misalin karfe 3 na rana (3pm) a babban filin Idin Bauchi domin gudanar da sallar jana’izar fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a ranar Alhamis.
Za a gudanar da jana’izar ne a babban filin Idi da ke Bauchi.
Babban aminin marigayin, Shariff Ibrahim Saley Al’husainiy, shi ne zai jagoranci sallar jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi kamar yadda Marigayin ya bar wasiyyar hakan. Ana sa ran jama’a daga sassa daban-daban na Afrika ne za su halarci wannan jana’izar.
A sanarwar da ya fito daga gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman, wanda M Daha Azhary Bauchi ya fitar ya shaida cewar, “Jana’izar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi….. Babban Amininsa Shariff Ibrahim Saley Al’husainiy, shi ne zai Jagoranci yi masa Sallah kamar yadda yyi Wasiyya.
“Za a yi Sallar ne a ranar Juma’a 28-11-2025 a babban filin Idi da ke Bauchi da ƙarfe 3:00 wato bayan Sallar Juma’a,” in ji M Daha Azhary Bauchi.






