Shigar Injiniya Sagir Ƙoƙi APC Zai Yi Tasiri A Karya Tsarin Kwankwasiyya A Kano -Bashir Baba Chilla

Daga Ibrahim Muhammad

An yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC su haɗa kansu, domin babu wata nasara da za a samu idan babu haɗin kai a tsakaninsu.

Hon. Bashir Babba Chilla tsohon Kantoman ƙaramar hukumar Birnin Kano da kewaye, Darakta Janar na tafiyar siyasar gidan Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi ɗan Majalisar Tarayya na ƙaramar hukumar Birni ne ya yi kiran da ya wakilci ɗan Majalisar taron shekara 23 da kafa ƙungiyar Maitaimako.

Ya ƙara da cewa kamar yadda kowa ya sani ne, sun fito daga jam’iyyar NNPP ne, kuma duk abin da aka yi tun daga kafa tsarin Kwankwasiyya zuwa ranar da suka fita daga cikinta sune suka yi, kuma sun san ya ake, dukkan hanyoyin da ya kamata su bi domin su karya tsarin su tabbatar da nasara sun sani, amma muhimmin abu shi ne su haɗa kansu a jam’iyyar APC nasara tana tare da su cikin yardar Allah.

Ya musanta zargin da ake yaɗawa na cewa ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano, Injiniya Sagir Koki shi kaɗai ya sauya daga Kwankwasiyya zuwa APC, ya tabbatar da cewa da su ya tafi, domin duk wanda yake Kwankwasiyya a Kano a ce masa Bashir Chilla ya san shi, domin shi kansa Kwankwaso ma shi ya karɓe shi a Kwankwasiyyar.

Ya ce maganar ka ce ɗan majalisar birnin Kano na Tarayya Sagir Ƙoƙi a ce ya fita shi kaɗai ba gaskiya ba ne, kuma lokaci zai nuna, yanzu ma a cikin tsarin gwamnatin jihar Kano da ƙananan hukumomi akwai wakilansu sun binne su tukuna suna nan, amma akwai ayyuka da za su yi daki-daki kowa ya san su ba sa yin siyasa ta harmagaza, kuma ba sa yin hatsaniya suna yi ne bisa tsari.

Ya ƙara da jadadda cewa duk mai cewa Sagur Ƙoƙi ɗan Majalisar birnin Kano na Tarayya shi ne ya bar NNPP shi kaɗai lokaci zai yi za a zo a karɓe shi a APC, za a ga da wa da waye suke tare da shi, amma dai komai lalacewa shekara 27 suna cikin tsarin Kwankwasiyya suka bar ta yau komai daƙiƙancinsu ya kamata mutum ya san suna da muhimmiyar rawa da za su taka, domin an faɗi da su a zaɓe an yi nasara da su, sun san yadda aka yi aka faɗi, kuma su suka fi kowa sanin yadda aka ci.

Hon. Bashir Chilla ya ce shigar da Injiniya Sagir Ƙoƙi ya yi jam’iyyar APC ba ƙaramin tasiri za ta yi ba, domin yanzu abin da yake gabansu ayyuka ne da cigaban mutane. “Ayyuka da yawa wanda ma muka yi a baya kamar ma ba mu yi komai ba ne. Za a ga kuma me za mu yi,” in ji shi.

Hon. Bashir Baba Chilla tsohon Kantoman na ƙaramar hukumar Birni da kewaye ya ce nan ba da jimawa ba Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi zai ƙaddamar da rijiyoyin burtsatse a mazabu 13 guda 16 da kayan abinci da za su raba ga masallatai na salloli biyar da ke ƙaramar hukumar Birni, za a bai wa Limamansu da Na’ibai da Ladanai. “Akwa ayyuka da yawa yanzu matasa za su sharbi romon damokaraɗiyya. Don haka ku kwantar da hankalinku, duk abin da za a yi na kyautatawa za a yi,” in ji shi.

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe