Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Kano Abdullahi Abbas ya nemi gafarar al’ummar Fagge game da maganganu da ake zargin na ɓatanci ne ga al’ummar abin da ya jawo fushi tare da shigar da shi ƙara a kotun Majistare da ke Kano.
An jiwo sautin neman gafarar ne da Abdullahi Abba ya yi a cikin wani sauti da Lauyan al’ummar Fagge, Barrister Abba Hikima Fagge, ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yake nuna cewa kuskuren fahimta aka yi masa a kan abin da ya faɗa. Ya ce shi ba shi da wata hujja ta wulaƙanta mutanen Fagge.
A kwanakin baya ne dai wasu mutum 10 cikin fitattun mazauna Fagge suka shigar da ƙara na zargin shugaban APC Abdullahi Abbas da yin kalaman ɓata suna da zai iya jawo tunzuri.
Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Dakta Nuruddeen Abubakar, Sheikh Abubakar Ya’u, Alhaji Sani Salisu da sauran mutane bakwai a madadin su da sauran mutanen unguwar da ke son zaman lafiya.
Masu ƙarar sun buƙaci kotu ta ba da umarnin a gayyaci Abdullahi Abbas ya bayyana a gaban kotu. Lauyoyin da suka shigar da ƙarar sun nemi kotu ta yi amfani da tanade-tanaden dokar ACJL 2019 domin umartar Kwamishinan ‘yan sanda na Kano ya binciki Abdullahi Abbas kan zarge-zargen da suka shafi cin mutunc da ɓata suna da neman haddasa ƙiyayya tsakanin wasu jama’a.
An ce maganganun Abdullahi Abbas sun fito ne yayin gudanar da wani taron siyasa, inda aka ji yana danganta “duk wani mara ƙima” da Fagge, tare da wasu ƙarin kalamai da mazauna yankin suka ce suna iya haddasa rarrabuwar kai.
Sai dai Abbas ya dage cewa an fassara kalamansa ba daidai ba, kuma bai yi nufin wulaƙanta wani ba.
Kotun Majistare na shirin yanke hukunci kan buƙatun da aka gabatar a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa, idan kuma an amince da haƙurin da ya bayar, hakan na nufin za a iya janye ƙarar.








