Daga Ibrahim Muhammad Kano
Kamfanin taki na “Solar Fertiliser” ya bayyana cewa a koyaushe suna aiki da dukkan ƙa’idoji da dokoki na Hukumar kula ingancin kaya ta ƙasa domin samar da kayayyaki masu inganci ga amfanin jama’a.
Manajan kamfanin taki na Solar Mista Yohana Ibrahim ne ya bayyana hakan a yayin taron ranar ingancin kayayyaki ta duniya da Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta ƙasa SON mai kula da shiyyar Kano ta gudanar a ranar Laraba.
Ya ce duk irin shawarwari da Hukumar ta ke ba su suna yin ƙoƙari su yi amfani da su da hakan kan tabbatar da gamsuwa da irin ingancin kayayyaki da suke.
Ya ce kamfaninsu na takin sola yana yin taki na NPK da sauran nau’uka na taki masu tasiri da ake amfani da shi a Arewa da kudancin Nijeriya da kuma ƙasashen maƙwabta da dama saboda yana da inganci a aikin noma.
Ya ƙara da cewa sukan bai wa manoma ma takin nasu su yi amfani da shi idan sun yi noma sai su kawo kuɗin domin yana ba su yabanya sosai, kuma da kansu suke dawowa su saya.
Mista Yohana Ibrahim Manajan kamfanin kamfanin na takin solar ya bayyana cewa duk mai harkar sarrafa kaya ranar ingancin kaya na da muhimmanci a wajen sa saboda ya zo ya nuna kaya duniya ta yi shaida kayansa yana da inganci.






