Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana ƙaramar hukumar Ghari da cewa dama tana da kyakkyawan tarihi a jihar Kano da ma ƙasa baki ßaya duk abin da ake na al’adun gargajiya har yanzu al’ummar yankin ba su bari ba.
Shugaban ƙaramar hukumar Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu ne ya bayyana hakan a yayin taron nuna al’adun gargajiya da aka gudanar a Kano.
Ya ce akwai abubuwa da suke yi na al’adun gargajiya musamman da kaka irin su kokawa, kalankuwa da wasan kamun kifi da sauran abubuwa na nishaɗi na al’adu na harkar mona.
Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu ya ce, “Don haka a wajen su wannan taro na nuna al’adu da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta shirya ake gudanarwa ya nuna cewa ana sane da mutanen karkara ana girmama al’adunsu. Wannan baje kolin al’adun zai jawo hankalin mutane daga ƙasashen waje ma, su zo yawon bude ido su ga irin al’adunmu.”







