Daga Ibrahim Muhammad
Taron nuna al’adu na taimakawa wajen farfaɗo da dukkan abubuwa da al’adu ana ƙara sani daga mutane daban-daban, hakan abin ƙarfafa gwiwa ne duba da al’ada madubi ne na al’umma da suke gani su yi alfahari da su.
Shugaban ƙaramar hukumar Doguwa Hon. AbdurRashid Rulwan Doguwar ne ya bayyana hakan.
Ya ce irin wannan taro da mutane daga ƙananan hukumomi suka zo suka baje hajar al’adunsu, kowacce da irin nata, wasu su ga na wasu su ma su ga nasu, za a ƙara kulla alaƙa da sada zumunci da wayar da kai domin kowa da al’adar sa yake ado ba sai ya aro daga wata ƙasa ba.
Hon. AbdurRashid Rulwan ya ce su a ƙaramar hukumar Doguwar suna alfahari da ƙasa mai kyau na noma da Allah ya ba su, babu wani abu da ba a iya noma shi a yankin, kuma suna da ma’adanai iri-iri da Allah ne ya san yawan adadinsu suna godiya ga Allah da ni’ima da ya ba su na arziƙin abinci kowane iri, kuma wannan irin taro da a karon farko gwamnatin jihar Kano ta gudanar zai daɗa fito da al’adun Doguwa a duniya.






