Daga Ibrahim Muhammad
Gyaran tsarin mulki da shigar da sabbin dokoki abu ne mai kyau da ya kamata a riƙa yi lokaci-lokaci saboda abubuwa na canzawa daga wani ƙarni zuwa wani.
Hon. Ɗankaka Husaini Bebeji jigo a jam’iyyar NNPP mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara a ofishin mataimakin Gwamna ne ya bayyana hakan.
Ya ce abin da aka yi a ba ya watakila ba zai yiwu ba a yanzu. Ya kamata a ce ana samun lokaci ana sake tattaunawa a sake duba irin dokokin da suka daɗe dace da ba su yi daidai da zamani ba a sauya su yadda za su amfani al’umma.
Hon. Ɗankaka Husaini Bebeji ya ce yana goyon bayan matsayin gwamnatin jihar Kano kan neman ƙarin ƙananan hukumomi da jiha 100 bisa 100 domin Kano an yi yawa, kuma ba ta samun adalci da ya dace a tsarin rabon albarkatun ƙasa.
Ya yi nuni da cewa domin yanzu akwai jihohin da suka fi Kano samun kuɗaɗe na gwamnatin tarayya da ba su kai girmanta ba, idan kuwa za a sami ƙirƙiro ƙarin jiha daga cikinta za a sami cigaba.
Hon. Ɗankaka Husaini Bebeji ya ce shi yana da ra’ayin a sa doka a tsarin mulkin ƙasa ma da ya shafi ‘yan siyasa, a yi gyaran tsarin mulki a hana ‘yan siyasa sauya jam’iyyar da aka zaɓe su a ciki ba har sai sun gama wa’adinsu.
Ya ce domin bai dace a zo a zaɓi wani a jam’iyya A ko B ko C ba sannan kuma ya yi tashin gwauron zaɓi, ya koma wata. “Wannan yana koyawa mambobi da aka zaɓa musamman Musulmi cin amana shi, kuma cin amana abu ne mara kyau. Duk abin da aka ce an zaɓe ka a wata jam’iyya ya zama komai rigimar da take ciki dole ka haƙura a haka har ka gama,” in ji shi.
Hon. Ɗankaka Husaini Bebeji ya ce idan da dama ka gama za ka sake shiga zaɓe ka shiga a jam’iyyar in babu dama wasu Allah ya kawo shi ke nan don sha’anin ba nasa ba ne shi kaɗai na mutane domin Allah da ya halicci kowa ya ba shi abin da zai yi iya rayuwarsa.








