Wajibi Ne Malamai Su Yawaita Jan Hankalin Matasa Kan Illar Shan Miyagun Ƙwayoyi -Gwamnan Kano

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kalandar Musulunci na shigowar sabuwar shekarar Musulunci a yayin taron murnar shiga sabuwar shekara da aka gudanar a rufaffen ɗakin wasanni na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a safiyar ranar Alhamis.

Taron ya sami halartar malaman addini da ɗalibai daga makarantun Islamiyya daban-daban a jihar Kano.

Shehin Malami Farfesa Umar Sani Fagge ne ya gabatar da jawabi a kan sabuwar shekarar Musulunci.

A nasa jawabin Gwamnan jihar Kano, wanda mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam ya wakilta ya ce wannan taro da ake ran 1 ga watan Muharram hijirar Ma’aikin Allah 1447, suna yi wa Allah godiya da ganin ranar da aka rufe shafin shekara 1446 wacce ta ƙare.

Ya yi nuni da cewa lokaci wani muhimmin al’amari ne a rayuwar ɗan’adam, shi ya sa Musulunci ke ba da muhimmanci a kan maganar lokaci, kowane al’amari da ɗan’adam yake ciki daga ranar da ya zo duniya zuwa ran da zai bar ta ƙididdigagge ne, ƙirgagge ne, aunanne ne, sananne ne wurin Mahaliccinsa. “Saboda haka ya kamata mu riƙa kula da lokaci da amfani da shi yadda za mu yi tutiya da irin abin da Allah ya haɗa mu da shi a wannan duniya,” in ji shi.

Mataimakin Gwamnan ya ce mai girma Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce a yi wa kowa barka da sabuwar shekara, kuma yana yi wa al’ummar jihar Kano fatan alheri a cikin wannan shekara da ta shigo da yi musu albishir na ƙara ƙoƙari wajen ƙara sama wa al’ummar jihar sauƙi da samar da kayayyaki na ingantuwar rayuwa.

Ya ce rana ce ta sabunta niyya na cigaba da fafutukar inganta ilimin addini da na zamani da inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyar al’umma da yaƙi da shanye-shayen ƙwayoyi da barnace-barnace da taɓarɓarewar tarbiyya ta matasa a wannan jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Rana ce da dukkannin mu za mu zage damtse wajen inganta harkokin tattalin arziƙi da harkar kasuwanci da Allah ya azurta Kano da su. Lokaci ne da ya kamata magidanta da matasa su zauna su yi wa kansu hisabi, su duba shekara da ta gabata mene ne riba da ƙalubale da aka samu, mene ne matakin ɗauka don tunkarar wannan shekara da aka shiga,” ya bayyana.

Mataimakin Gwamnan ya ja hankalin masu ruwa da tsaki tun daga kan malamai da ‘yan siyasa da masu mulki su riƙa wayar da kan al’umma don ɗora matasa a kan turba ta gaskiya da za su zama masu amfani don maganin jafa’in da ake wa jihar Kano na cewa ta fi kowace jiha a ƙasar nan yawan masu shan ƙwaya a ƙasar nan. Shi ya sa ake kashe mutane wajen ƙwatar waya.

Ya ce ya kamata a sa ido a ga yadda za a kau da wannan shaƙiyancin da a fahimtarsa wata dasisa ce ta musamman daga wasu mutane daga wasu wurare ake zuwa ake dasa mana ita a cikin wannan al’ummar. “Muna da labarai iri-iri a cikin masu wannan dasisa har akwai masu bai wa yara ƙwaya kyauta in sun ga ba su da kuɗin saye za su ba su su sha, saboda kar su rabu da ita, za su yi sata, za su yi kisa za su yi su zo dai su saya ba abin da ya dame su ba ne.

Ya nuna cewa a matsayin jihar Kano na birni mai karɓar baƙi ba yana nufin komai aka ga dama kuma sai a yi ba. “Muna fatan haɗa ƙarfi da ƙarfe da ma’aikatar kula da addinai da hHkumar Shari’a duk abin da ake so a ɗura ya shiga har ƙasa cikin lungu ya shiga gidaje har ɗakuna suna da hanyar da za su tura a kai har ciki,” ya ce.

Ya ƙara da cewa wannan masifa ta ƙwaya da kashe-kashen nan ba gaira babu dalili masifa ce ta gaske da bai kamata su yi wasa da ita ko a raina ta ba, birane irin ƙasaitaccen birni na Kano akan yi fama da matsaloli irin wannan, lokuta-lokuta tun tale-tale duk tsofaffin birane irin wannan ana himma da sa ido don tabbatar da cewa ba a zurawa abubuwa ido an ƙyale su sun tafi sakaka ba shi ne zai tabbatar da tsarewa da kulawa da tsaftace matasa daga bala’o’i da irin wannan yanayi ke haifarwa.

Ya yi kira ga limamai a kan su yawaita jan hankalin mutane a huɗubobi da suke yi, musamman ga matasa da iyaye da shugabanni na masarautu da ‘yan siyasa a kan muhimmancin zaman mu lafiya ‘ya’yammu su ‘yantu ba sa shan ƙwaya duk yaron da aka haɗa da ƙwaya an rusa shi, an rusa rayuwarsa. “Duk al’ummar da matasanta suka lalace da ƙwaya ta tasamma rushewa. Ya kamata a yi da gaske a kan yaƙi da shan ƙwaya a wannan sabuwar shekara ta Musulunci da muka shiga da muke fata cikin hukuncin Ubangiji za mu sami gagarumar nasara wajen yaƙi da shan ƙwaya da masu sayar da ita ko daga ina suke, ko su waye a cikin jihar Kano. Wannan aiki ne na kowa. Sai iyaye da shugabanni musamman malamai domin su nasu na musamman ne, sune idan suka faɗa wa al’umma magana take shiga har zuci ta yi tasiri, shi ya sa yake ta magana a kan majalisar malamai da ta islamiyyu da majalisar limamai da ma’aikatar kula da addinai da Hukumar Shari’a ta jiha, in ji Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, shugaban Hukumar Shari’a ta jihar Kano, Malam Abubakar Daneji ya ce, shekara da shekaru ba a taɓa samun nasara irin na wannan lokaci ba da Gwamnan jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba su goyon baya da gagarumar gudunmawa suka yi ƙoƙari wajen ƙaddamar da kalandar Musulunci a ranar 1 ga watan Muharram.

Ya ce domin a gwamnatin shekarun baya sai a shafe wata uku, huɗu har shida ma ba a gabatar da kalandar ba, amma cikin yardar Allah da ikonsa aka ƙaddamar da wannan kalanda a daidai farkon ranar sabuwar shekarar Musulunci ta 1447.

Shugaban na Hukumar Shari’a, Malam Abubakar Daneji ya ce Hukumar su a shirye take ta taimakawa ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano wajen kawar da faɗan daba da ƙwacen waya a Kano domin Musulunci ya yi umurni wanda duk ya ga wani abu da ake ba daidai ba ya yi ƙoƙari ya hana, su a hukumarsu ta shari’a da yardar Allah za su haɗu da jami’an tsaro domin hana wannan abu shi ya sa suka gayyaci dukkan jami’an tsaro da suke bayar da gudunmawa mai yawa don ba za su zuba musu ido a ce su kaɗai za su yi ba su ma a matsayinsu na malamai masu faɗakarwa da addu’a za su fito da hikimomi da dabaru daban-daban da za su yi su, kuma haɗa da iyayen yara da masu unguwanni da limamai da duk wanda ke da hannu wajen tarbiyyar al’umma domin cimma nasara.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun