An Kashe Fiye Da Yaran Turji 100 – Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Yaran Bello Turji Fiye Da 100

A wani ƙoƙari na murƙushe ta’addanci da Gwamna Dauda Lawal yake yi, Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da kashe sama da mutane 100 masu biyayya ga fitaccen shugaban ’yan ta’adda, Bello Turji, a wani samame na haɗin gwiwar jami’an Askarawan Zamfara (CPG) suka kai maboyar ’yan ta’addan da ke dajin Cida a ƙaramar hukumar Shinkafi.

Mataimaki na musamman kan harkokin tsaro ga Gwamnan Zamfara, Alhaji Ahmad Manga ne ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa.

Sun ƙaddamar da harin ne da gudunmawar wani tubabben ɗan bindiga, Bashari Maniya wanda ya jagoranci kai farmakin a kusa da ƙauyen Cida na ƙaramar hukumar Shinkafi.

Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.

Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne.

“Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga.

Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka kashi mutanensa, wanda shi kansa bai iya ƙididdige abin da ya rasa, sai dai daga baya”.

Ya ce duk inda ka ga gawawwaki to akasari na yaransa ne.

Mataimaki na musamman kan sha’anin tsaron ya ce Bashari Maniya ya gamu da ajalinsa ne sakamakon hatsarin da motarsu ta yi lokacin da ta faɗa wani rami.

“Sabuwar mota ce wanda ba duk mutum ya san kanta ba, sun taka wani rami ne mai kama da rijiya kuma suna a guje, motar ta ƙwace kuma ta je ta faɗi. Ba wai shi ne ya yi nasarar buge motar ba, a’a.”

Ya ƙara da cewa lokacin da aka kai musu ɗauki an samu Maniya da sauran waɗanda ke cikin motar ne ba a hayyacinsu ba, saboda motar harbi ba ya ratsa ta.

Alhaji Ahmad Manga ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Zamfara za ta ci gaba da farautar Bello Turji ba rdare ba rana.

“Wallahi sai abin da ya ci gaba. Alhamdulillahi! Duk ɗan jihar Zamfara zai gaya maka musamman ɗan yankin Shinkafi sun sani, abin da aka yi shekara 14 yana gallaza wa mutane. Shi ya san rawar da jami’an tsaro suka taka yanzu ba a taɓa isko shi ba, irin yadda aka tarad da shi har gidansa.

Ya bayyana aniyar gwamnatin Zamfara na shigo da ƙarin dakarun sojoji don ci gaba da tunkarar Bello Turji

A cewarsa, ko a faɗan da aka yi ranar Litinin Bello Turji laɓewa ya riƙa yi, kafin daga bisani ya arce.

Related Posts

Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo