WOTCOSA Ajin 1975 A Shekara 50: Sun Karrama Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje Da Tagwayen Lambobin Yabo

Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban tsohuwar makarantar horon malamai ta mata ta Kano (WTC), Women Teachers College Old Girls Association (WOTCOSA) da yanzu ake kiran a makarantar da Goverment Girls College (WTC) Kano ‘yan aji na 1975 sun gudanar da taron cika shekaru 50 da kammala makaratar.

Taron tsofaffin ɗaliban da aka gudanar a harabar makarantar ranar Talata ya haɗa da buɗe ɗakin karatu makarantar da aka gyara aka sanya littafai da fitilu da fankokin masu aiki da hasken rana da kujjeru da kuma gyara masallacin makarsntar da mai ɗakin tsohon Gwamnan jihar Kano tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban ta ɗaukin nauyin yi.

A yayin taron, ƙungiyar ta WOTCOSA ta karrama Uwargidan Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da tagwayen lambobin yabo bisa irin ɗimbin gudunmawa da take bai wa cigaban ƙungiyar da makarantar tasu da harkar ilimi da kuma irin karamci da jinkan al’umma.

A jawabinta a taron, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa taron nasu abin jin daɗi da farin ciki ne, suna gode wa Allah bisa yarjewa da ya yi har yanzu suna tare da juna da zumunci tsakaninsu wanda hakan rahama ne daga Ubangiji da ya yi a gare su, domin wasu ɗaliban idan an gama makaranta an watse ke nan sai dai a haɗu a hanya a gaisa.

Ta ce yanzu irin zumunci da suke da shi a tsakaninsu suna halartar bikin aure da suna a tsakaninsu yaransu da suka taso in lokacin aure ya yi suna haɗuwa ana buki ta kai wa juna ziyara. “Yanzu har na jikoki ake zuwa. Muna godiya ga Allah da ya bar mu da rai da lafiya, ya ba mu iko muka yi tattaki na kusa da na nesa suka zo makarantar da suka gama shekaru 50,” in ji ta.

Farfesa Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta ce duk wani abu da yake faruwa Allah ne yake ƙaddarawa ya yi amfani da bawa wajen taimaka wa al’umma, kuma irin abin da suke tarbiyya ce da suka tashi da ita daga iyaye da kakanni, kuma Allah ya taimaka ya ba ta mai gida kamilalle, bawan Allah, Dakta Abdullahi Umar Gandije da suka zauna tare suka ƙirƙiro Gidauniyar Ganduje da a ƙarƙashinta suke kyautata wa al’umma, kama daga gina masallaci da makarantu, musuluntar da Maguzawa da kula da harkar lafiya a fannoni daban-daban a wannan ƙarfin gwiwa ne da Allah ya ba da shi da kulawar iyaye.

Ta yi nuni da cewa a baya can iyayensu sun hango inganci na karatu lokacin da aka zazzaɓo su aka kawo su makaranta duk da ana nuna damuwa a kan tura yara karatun boko a lokacin don fargabar kada su rasa tarbiyya, amma iyayensu suka gane neman ilimi da mace da namiji duk abu ne mai muhimmanci, kuma ya danganta da yadda aka ɗora tarbiyyar yaro a gidansu.

Ta yi kira ga iyaye a kan su tashi tsaye su sanya ido a kan tarbiyya ‘ya’yansu maza da mata tun suna ƙanana saboda a abokantaka a da su iyayensu sun san gidan da yaro zai tafi an san wajen da zai je, in wani ya zo an san ɗan wane gida ne ya zo, amma yanzu kula da hakan abin ya yi sauƙi, dole a yi waiwaye abin nan na baya da aka bari a baya na kyautata tarbiyya a dawo da shi don inganta tarbiyyar yaran al’umma, “Domin yaran nan sune arziƙi da za mu yi alfahari da su, ya kasance sun hau hanya yadda ya kamata su riƙe ilimi na addini da na zamani. Kowa na da gudunmawa da zai bayar,” ta jaddada.

A nata jawabin Shugabar tsare-tsare ta kwamitin gudanar da taron cika shekaru 50 na WOTCOSA, Hajiya A’isha Ja’afar Yusuf ta ce, wannan buki gagarumi ne duk da ba shi ne na farko ba da tsofaffin ɗaliban makarantar ajin 75 suka yi ba.

“Mu da muka yi makarantar mafi yawa mun yi malanta na aji da yawanmu mun yi mataimakin shugaban makarantun Sakandare da na shugabannin Firamare har Allah ya kai mafi yawanmu zuwa manyan matsayi duk a tafarkin koyarwa,” in ji ta.

Ta ce duk wanda aka ce yau yana cika shekaru 50 da gama makaranta abin godiya ne ga Allah, don makarantar ta yaye ɗaliban da suka zama manyan mutane.

Ta gode wa malamansu da suka riƙe su a lokacin ajujuwa biyu ne ma yawanci kowane aji mutum 20 zuwa sama ne a ciki ba ya kai wa 30 akwai lokaci na kulawa da yara sosai malamansu Turawa ne ma mafi yawa.

Ta ce daga ɗalibai yan ajinsu akwai matar Dakta Abdullahi Umar Ganduje tsohon Gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da wata matar wani Gwamnan ma da Farfesoshi da manyan Likitoci, Lauyoyi, ‘yan siyasa da ɗalibai da dama da suka kan manyan matsayi a fagage da dama.

Hajiya A’isha Ja’afar Yusuf ta ƙara da cewa akwai wani taro da suka taɓa yi a baya suka kira shi ‘ka dawo da kujerarka,’ saboda a shawo kan ƙarancin abin zama a makarantar da Farfesa Hafsat ta ji ita ta yi wa duka ajin kujeru guda 60 sai ta zo ta bai wa makarantar gadaje da katifu har da kuɗi tana yin abubuwa da yawa a makarantar.

Hajiya A’i’sha Ja’afar Yusuf yi nuni da cewa shi tarbiyya daga gida ake farawa don haka ta yi kira ga iyaye su jajirce a kan tarbiyyar ‘ya’yansu in sun je makaranta malamai ne suke ɗawainiya da su idan sun koma gida iyaye su sa ido domin zamani ya canza, kuma Allah ya halicce mata su kula da tarbiyyar da tsaftar yara a gida su ba su ilimi, domin shi ilimi in babu tarbiyya shirme ne. “In aka gino tarbiyya daga gida sai ɗaliba ta zo sauran yara ma su ƙaru,” ta ƙarƙare.

  • Related Posts

    Ɗaliban Ƙaramar Hukumar Dala Da Gwamnatin Kano Za Ta Tura Manyan Jami’o’i Na Cikin Gida Da Ƙasashen Waje Karatun Digiri Na Biyu, Sun Yi Taron Nuna Godiya

    Daga Ibrahim Muhammad Ɗalibai ‘yan asalin ƙaramar hukumar Dala da za su tafi karatu manyan jami’o’i a ciki da wajen ƙasar nan da gwamnatiin jihar Kano ta ɗauki nauyinsu sun…

    Muna Sauya Zamfara Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na gina jihar da ke tafiya bisa tsarin zamani mai dogaro da fasahar zamani. A ranar Talata, gwamnan ya buɗe shirin…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe