Ya Kamata A Ba Da Gudunmawa Sosai Wajen Cigaba Da Bunƙasa harshe, tarbiyya da al’adar Hausawa a Duniya -Hajiya Hauwa’u Abdulkarim Yaufaniya

Daga Ibrahim Muhammad

An yaba da irin ƙoƙarin da wata Gidauniya take na haɗa kan Hausawan Duniya domin yunƙurin mai muhimmanci da zai daɗa bunƙasa mutuncin al’ummar hausawa.

Hajiya Hauwa’u Abdulkarim Yaufaniya, wata ‘yar jaridar ƙasar Ghana da ta yi aiki da sashen Hausa na Muryar Amurka ce ta wannan yabon da take zantawa da ‘yan jarida ba bayan taron.

Ta ƙara da cewa taron Gidauniyar da ta halarta a Kano ya ƙarfafa mata gwiwa sosai a matsayinta na Bahaushiya ‘yar asalin ƙasar Ghana ya tabbatar mata da riƙe harshen Hausa wanda shi ne asalinta da ta yi a Ghana wani abu ne mai muhimmanci da take alfahari da shi a duniiya.

Hajiya Hauwa’u Abdulkarim Yaufaniya ya ce irin wanan taro ya kamata a ba shi muhimmanci sosai a duk inda ake amfani da harshen Hausa, musamman wajen riƙe al’adu musamman ma a yanzu da duniya take sauyawa ana amfani da fasahar zamani.

Ta ce yana da kyau kowane Bahaushe matashi da matashiya har ma da iyaye kowa ya koyi wani abu dangane da wannan fasaha ta zamani, idan kuma ka samu kanka dama kana anfani da shafukan sada zumunta ka yi aiki don ka kyautata harshen Hausa da al’adunta, ka nuna wa duniya kai Bahaushe ne ga yadda al’adarka take.

Ta yi nuni da cewa harshen Hausa na daga manyan harsuna da yake saurin yaɗuwa a duniya. Ya zama kamar yadda Indiyawa da Sinawa da Turawa na Gabas da Yamma su ke nuna al’adunsu da yanayin zamantakewarsu mai kyau, kai ma Bahaushe ka nuna wa duniya ga irin naka al’adun.

Don haka ta ƙara jaddada kira ga matasa da masu harkokin finafinai na Hausa gaba ɗaya su yi kishin Hausa da al’adarta, su riƙa ɗaukar wannan ɓangaren suna amfani da shi a fim domin mutane a duniya su fahimci cewa Hausa wata al’umma ce da take da tarbiyya da kunya da al’adu masu kima da ban sha’awa don a kwaikwaya.

Hajiya Hauwa’u Abdulkarim Yaufaniya ta ce masu harkar fim za su iya ba da gudunmawa sosai wajen sawa al’adun Hausa su yi tasiri a rayuwar mutane ko da ta irin shigar sutura da za su yi ta sanya kayan al’ada da nuna tarbiyya da kyakkyawan mu’amala da mutane za su yi saurin gane Bahaushe ya kamata kowane Bahaushe ya zama mai isar da wannan saƙo a duk inda ya sami kansa.

  • Related Posts

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Daga Ibrahim Muhammad An kammala bikin rufe Baje Kolin Duniya na 46 da Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Kano (KACCIMA) ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Usman Darma, a yammacin Asabar.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe