Daga Ibrahim Muhammad
An yi kira ga matasa a kullum su riƙa ƙoƙarin koyon sana’o’i na dogaro da kai maimakon su tsaya suna jira wani ya ba su. Wannan ba abin da da ya dace ba.
Alhaji Jibrin Musa Muhammad da aka fi sani da Acaska Yaron Birni ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a taron rabon tallafi da Abban Gandu ya gudanar.
Ya bai wa matasa shawara da cewa dole idan suna so wani abu su same shi sai suna yi ƙoƙarin yin wani abu na kansu na sana’o’i, sannan sai a gani a tallafa musu, “Amma ba za ka ce ba ka da komai ba, kuma ka ce wai wani kake jira sai ya zo ya ba ka kullum. Wannan ba dabara ba ce, kashe zuciya ne.
“Don haka matasa su tashi su nema, idan kana da wani abu wanda kake ganin za ka yi in ka tashi tsaye kana yi kake tunanin wani wanda zai taimake ka ya gani kana da sana’a ka ce so kake ya tallafa maka, to zai fi jin ƙwarin gwiwa ya tallafa maka domin kamar kama-kama ne za a yi a ɗora wa mutum kaya aka, sai ya kama na a kama masa can sai a ɗora masa ya ɗauka, haka rayuwa take,” in ji shi.
Alhaji Jibrin Musa Muhammad ya ce, maganar a ce matasa sun yi karatu na zamani ko na addini mai zurfi wannan ba dalili ba ne su zauna su ce sai gwamnatin ta ba su
aikin yi don Annabawa da Allah ya aiko suna sana’a, akwai wanda yake kiwo, akwai mai noma, akwai mai ƙira, akwai mai kasuwanci. Saboda haka don ka yi karatu an wuce lokacin da za ka yi jiran gwamnatin ta zo ta yi maka. Ya kamata ka tashi ka ƙirƙiro wani abin da kai ma kana kuma ɗaya za ka iya ɗaukar 10 ka yi wannan harkar da su.
Ya ba da misali da cewa kamar shi ɗan kasuwa ne, kuma ya yi karatu, kuma kamar yadda aka sani mahaifinsa ɗan boko ne ya yi siyasa, har ya yi Sanata. Don haka shi ma yanzu yana siyasa, kuma ɗan kasuwa ne da a yanzu haka yana da mutane da suke aiki a ƙarƙashinsa da yake biya aƙalla sama da mutum 100. Duk da ya yi makaranta bai taɓa yin aikin gwamnati ba, bai dogara da sai ta ba shi aiki ba.
Ya ce kamar Abba Aliyu Gandu ba kawai ‘yan unguwarsu ta Gandu yake wa tallafi ba, yana fita wasu unguwanni yana ba da tallafi don ƙarfafa gwiwar matasa da mata a kan sana’a, kamar wanda ya yi na ₦10,000 mace akwai abubuwa na sana’a da za ta iya yi da su a cikin gida da waɗannan kuɗaɗen za su riƙa ƙaruwa har su zama babban jari. “Idan kana yin sana’a da iya abin da kake da shi, in za ka dage ka nema, Allah zai sa maka albarka a ciki,” ya bayyana
Alhaji Jibrin Musa Muhammad Acaska Yaron Birni, ya yaba wa irin ƙoƙarin da Abba Gandu yake da irin abubuwan da yake da su ake suna gani, kuma irin wannan tallafi domin dogaro da kai da yake yanzu ma aka fara. Akwai na ƙarin dimbin abubuwa da za su riƙa ɓullowa su, kuma da suke a matsayin ƙannensa sai su ce masa Allah ya saka masa da alheri domin daidai gwargwado yana yin iya abin da zai iya, domin akwai mutane da yawa da suka sami dama, amma ba su zo sun yi wa al’umma tallafi irin wannan ba, amma shi tun kafin ya samu muƙami ma yana yi, yanzu da ya samu ya sake fitowa yake yi wa mutane ba abin da za su ce sai Allah ya saka da alkhairi.








