Za Mu Cigaba Da Ba Gwamna Abba Kabir Yusuf Goyon Baya -Shugaban Kungiyar Ƙwadago

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Kano, ta bayyana cewa za ta cigaba da goyon bayan Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf a kan irin ayyukan da kyawawan manufofiin da yake aiwatarwa ga ma’aikata da al’ummar Kano baki ɗaya.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da goyon bayan ma’aikatan ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025.

An dai gudanar da bikin ranar ma’aikata ta duniya ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a ranar Alhamis, 1 ga
Mayu, 2025..

Kwamared Kabiru Inuwa, ya yi nuni da cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa tarihi a matsayin shi ne Gwamna na farko a faɗin ƙasar nan da ya soma aiwatar
da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na N71,000

Ya bayyana hakan da cewa jarunta ce da Gwamnan ya nuna, kuma ya cancanci a yaba masa a kai domin hakan ya taimaaka wajen rage wa
ma’aikata raɗaɗin halin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziƙin da suke ciki.

Kwamared Inuwa ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir ya zo ya yi ƙarin mafi ƙarancin fansho daga N5,000 zuwa N20, 000 da kuma biyan kuɗaɗen garatuti da ake bi bashi a gwamnatocin baya. “Wannan mataki ne da ke nuna kulawar Gwamnan ga tsofaffin ma’aikata,” in ji shi.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ya taɓo ayyuka da dama da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa domin bunƙasa cigaban al’ummar jihar Kano da kuma ma’aikata a ɓangarorin ilimi da lafiya da sauran fannonin.

Kwamared Kabiru Inuwa ya ce ma’aikatar jihar Kano a shirye suke su cigaba da bai wa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf haɗin kai da goyon baya a kan kyawawan manufofinsa na ciyar da jihar gaba.

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe