Daga Ibrahim Muhammad
An rantsar da sabon kwamitin riƙo na shugabancin ‘yan kasuwar Kantin Kwari da ke Kano a ƙarƙashin Alhaji Abdullahi Shariff Namalam da zai jagoranci ƙungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.
Taron rantsuwar an gudanar da shi ne a Ma’akatar Kasuwanci ta jihar kano ranar Talata ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar Alhaji Shehu Wada Sagagi ya sami halartar dinbin ‘yan kasuwar.
Sagagi ya nemi ‘yan kasuwar su haɗa kai da kamfanonin ƙasashen duniya da suke mu’amala da su don jawo hankulansu wajen samar da wasu abubuwa da za su tallafawa cigaban kasuwanci da horar da matasa a kan yadda za su amfani cigaban kasuwanci a jihar Kano.
A jawabinsa, Manajan Darakta na hukumar kasuwar Kantin Kwari, Hon. Hamisu Sa’ad Dogon Nama ya ce, suna da kyakkyawar dangataka da ‘yan kasuwar, kuma su ma ‘yan kasuwa ne ba baƙi ba, illa dai kawai shi yana wakiltar gwamnati ne a kasuwar.
Ya ƙara da cewa su kuma ƙungiyar ‘yan kasuwa na wakiltar ‘yan kasuwa ne, don haka dukkansu abokan mu’amalar juna ne wajen gudanar da al’amuransu.
“Ita kasuwa tana ɗauke da al’umma ne, kuma doka ta yarda su yi ƙungiya don kare muradunsu a matsayinsu na ‘yan kasuwa,” in ji shi.
Manajan Daraktan na hukumar gudanarwar kasuwar Kantin Kwari, Hon.Hamisu Sa’ad Dogon Nama ya ce, ƙungiya tana da muhimmanci, ita take wakiltar ‘yan kasuwa, “Domin a Kantin Kwari akwai ‘yan kasuwa sama da miliyan, idan gwamnati tana da wani abu, ba sai ta tara su ba, ta hanyar ƙungiya za ta yi magana da su. Su ma idan suna da buƙata a wajen gwamnati ta ƙungiya za su isar ita za ta zama a tsakiya ne tsananin ‘yan kasuwa da gwamnati,” ya jaddada.
Shi ma a nasa jawabin, sabon Shugaban kwamitin riƙo na shugabancin ƙungiyar kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Abdullahi Sharif Namalam ya ce, samar da wannan kwamiti wani abin tarihi ne ga kasuwar, suna kyautata zaton in Allah ya yarda wannan tsarin da aka zo da shi, Allah zai fitar da su kunya.
Ya kuma yaba da irin albishir ɗin da Kwamishinan Kasuwanci ya yi musu na cewa gwamnatin jihar Kano za ta kawo tsare-tsare na bunƙasa cigaban kasuwar, za su mara mata baya domin tabbatar da nasara da yardar Allah.
Alhaji Abdullahi Sharif Namalam ya ce burinsu a ƙarƙashin kwamitin su sami haɗin kai daga hukumar kasuwar da ƙananan ‘yan kasuwa da manya a kasuwar Kantin Kwari domin cigaban kasuwar.






