Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana zaman aure da cewa abu ne da sai an yi haƙuri da juna, musamman in aka yi la’akari da yadda zaman yake sauyawa.
Alhaji Abdulrahman Badaru Abubakar, ɗaya daga cikin ‘ya’yan ministan tsaron Nijeriya ne ya bayyana haka ne bayan ɗaurin auren ‘ya’yan ministan tsaron Nijeriya; Zainab Hadari Abubakar da Sadiya Badaru Abubakar da aka gudanar a masallacin Alfurƙan a Kano ranar Juma’a.
Ya ƙara da cewa suna mutuƙar godiya da farin ciki sosai da zuwa da aka yi don shaidar wannan ɗaurin aure da aka gudanar na ‘ya’yan ministan tsaro na Nijeriya, Alhaji Badaru Abubakar mutane sun zo daga sassa daban-daban suna fata Allah ya sanya albarka da alheri ga auren.
Abdulrahman Badaru Abubakar ya yi nuni da cewa, amsa gayyata da taruwar ɗimbin mutane bai ba su mamaki ba a matsayinsu na ‘ya’yan tsohon Gwamnan jihar Jigawa, ku ma ministan tsaron Nijeriya domin mahaifinsu mutum ne na mutane da ya ba da gudunmawa ga cigaba a lokacin da yake Gwamna, kuma yanzu ma yake bayarwa ga cigaban ƙasar nan gaba ɗaya a matsayinsa na minista.






