Zan Yi Aiki Tuƙuru Domin Sauke Nauyin Da Gwamnan Jihar Kano Ya Ɗora Min -Saleh Musa Sa’ad Wailare

Daga Ibrahim Muhammad

Mai bai wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf shewara na musamman a kan hidimtawa al’umma Dakta Saleh Musa Sa’ad ya bayyana cewa zai jajirce da yin aiki tuƙuru a kan muƙamin nasa domin cimma nasara.

Ya ce wannan ofis da Gwamnan Jihar Kano ya ba shi zai dage ya ga ya jajirce saboda yarda da ya yi da shi ya ga ya jawo mutane daga masu zaman kansu da hukumomin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyi na duniya da na cikin gida da masu hannu da shuni don tallafawa bunƙasa cigaban al’umma.

Ya yi nuni da cewa matasa akwai abin da suke kallo daga wannan matsayi da Gwamnan Kano ya ba shi, shi ya sa suke murna da muƙamin, don haka zai yi aiki tukuru da za su amfane da za su fito a ɗaruruwansu lokacin zaɓe mai zuwa na 2027 domin tabbatar da nasara.

Dakta Saleh Musa Sa’ad Wailare mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara na musamman a kan hidimta wa al’umma ya ce za su yi aiki da ƙwarewa bisa gaskiya da amana, domin sauke nauyi da aka ɗora musu na cimma manufofin Gwamnan jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf na kyautata cigaban jihar Kano.

Kafin naɗa shi a wannan muƙami Dakta Saleh Musa Sa’ad Wailare ya kasance ɗan siyasa, jigo a tafiyar Kwankwasiyya a ƙananan hukumomin Ɗambatta da Maƙoda mai ƙoƙarin hidimtawa cigaban al’umma da yake bayar da gudunmawa wajen bunƙasa cigaban matasa maza da mata da sauran al’umma ta tallafa musu a kan harkar ilimi da sama musu ayyukan yi a hukumomin gwamnati da kamfanoni da ɗora su a kan sana’oi na dogaro da kai.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala. A yayin ziyarar, ƙungiyar…

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Ƙungiyar Jaruman Kannywood Sun Kai Wa Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala Ziyarar Girmamawa

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    Mata Su Dage Wajen Karatun Fannin Zayyana Gine-Gine (Architecture) -Arc. Binta Ahmad Umar

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    An Buɗe Sabon Masallacin ’Yan Nama a Kasuwar Sabon Gari, Kano

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Why I Cannot Approach the Court on the Bekwarra LGA Matter?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?