Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Hukumar Binƙasa Arewa Maso Yamma, ƘarƙashinSanata Babangida Husain Sunyaba Cigaban Da Aka Samu Na Kafa Hukumar

Daga Ibrahim Muhammad

Kwamitin ‘yan majalisar Dattawa mai kula da Hukumar Bunƙasa Cigaban Arewa maso Yamma ƙarƙashin jagorancin Sanata Babangida Adamu, sun ziyarci mazaunin Hukumar da ke jihar Kano bayan watanni shida da kafa ta.

A lokacin ziyarar, Sanata Babangida Husaini ya yaba da yadda ya ga aikin ke tafiya, tare da cewa za su riƙa zuwa ziyarar lokaci zuwa lokaci don ganin al’ummar yankin sun ci gajiyar Hukumar.

Ya ƙara da nuna gamsuwa kan gwadabe da aka biyo da za a kai ga biyan buƙata da ake sa rai na tabbatar da cin moriyar Hukumar ga al’ummar Arewa maso Yamma.

Sanata Babangida Husaini ya gode wa shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tunibu bisa amincewa da ƙirƙirar Hukumar, tare da gode wa mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau .I Jibrin da shi ne ya fitar da ƙudirin tun da fari, ya yi ƙoƙari matuƙa wajen tabbatar da Hukumar, ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kano da ta ba da sabbin motoci da wuri da za a gina ofishin dindindin na Hukumar.

A nasa ɓangaren shugaban Hukumar Bunƙasa Cigaban Arewa Maso Yamma, Farfesa Shehu Abdallah Ma’aji ya bayyana jin daɗinsa bisa ziyarar da kwamitin Majalisar Dattawan ƙarƙashin Sanata Babangida Husaini suka kawo a manyan gine ginensu guda biyu wanda Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u ne ya ba su da kuma shugaban Jami’ar Maryam Abacha Farfesa Adamu Gwarzo suka bayar, kuma aikin na tafiya kan tsarin da aka tsara a kai, kuma sun yaba.

Shugaban Hukumar Farfesa Shehu Abdallah Ma’aji ya gode wa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa katafaren fili hekta biyu da ya ba iwa Hukumar domin gina mazauninta na dindindin.

Farfesa Shehu Abdallah ma’aji ya yi kira ga dukkan masu kishin cigaban Arewa da cewa an ba su ƙalubale a kan Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma da sauran shiyyoyi. Don haka su tashi su ba da gudunmawa don cimma nasara a kai.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo