Daga Ibrahim Muhammad
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi ya yi naɗe-naɗen sarauta guda biyar a fadarsa, ciki har ɗansa Alhaji Adam Lamiɗo Sanusi da ka naɗa Tafidan Kano.
Tun da farko bayan naɗin, Alhaji Muhammad Sanusi ya bayyana cewa an yi wa Adam Lamiɗo Sanusi naɗin na matsayin Tafida ne a masarautar bisa la’akari da irin ƙwazo da tarbiyya da himmarsa a wajen neman ilimin addini da na zamani da ƙoƙarin kawowa al’umma cigaba.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan naɗin nasa, Tafidan Kano Alhaji Adam Lamiɗo Sanusi ya gode wa Allah bisa wannan yarda.da mahaifinsa ya yi masa har aka naɗa shi wannan sarauta mai girma a masarautar Kano. Sannan ya yi fatan Allah ya ba su iko na sauke nauyin.
Ya ƙara jaddada godiya ga iyaye da masoya waɗanda suke nuna masa ƙauna har aka kai ga wannan matsayi da kuma mutane da suka zo daga wuraren daban-daban suka taya shi murna .
Haka kuma ya miƙa godiya ga Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da wannan matsayi, tare da yin addu’a gare shi da mahaifinsa Sarkin Kano. Allah ya taimake su ya biya buƙatunsu, ya karya maƙiyansu na sarari da na ɓoye.
Alhaji Adam Lamiɗo Sanusi ya ce daga cikin abubuwa da yake tsarawa akwai shiri da ake na tallafawa mutanen Kano ta ƙarƙashin wata Gidauniya da ya kafa. Sannan suna ƙoƙarin haɗa kai da gwamnatin Kano don kawo harkar lantarki da a yanzu ma batun ya yi nisa har waɗanda za su sa hannun jari sun zo Kano nan ba da jimawa ba cikin yardar Allah za a kai ga nasara.
Tafidan na Kano, Alhaji Adam Lamiɗo Sanusi ya yi alƙawarin cewa zai yi aiki tuƙuru wajen kare martabar Musulunci da masarauta da al”ummar Kano a duk inda yake, kuma zai cigaba da yin koyi da irin kyawawar tarbiyyar da mahaifinsu mai martaba Khalifa Muhammad Sanusi ya ɗora su a kai.






