Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar masu tuƙa motocin ƙurƙura da mamallakansu a jihar Kano, ta ja hankalin Gwamnati da ta yi taka-tsantsan wajen shirin dawo da tsarin sanya traka a ababen hawa, da nufin inganta tsaro.

Ƙungiyar, wadda ake kira Union of Kurkura Drivers and Owners Association, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sani Abdul Muɗallib Maisalati, ta bayyana damuwarta kan yadda gwamnati ke shirin sake aiwatar da tsarin, ba tare da cikakken bayani ko tuntuɓa da shugabancin ƙungiyar ba.

Mambobin ƙungiyar sun koka da cewa a gwamnatocin da suka gabata an yi yunƙurin sanya traka har sau biyu, inda aka karɓi kuɗaɗe daga masu motocin kurkura, amma daga baya aka dakatar da shirin ba tare da an kammala shi ba, kuma ba tare da an mayar musu da kuɗaɗen da suka biya ba.

Sun ce wannan ne ya ƙara musu fargaba game da sabon shirin da ake shirin aiwatarwa.

Sun bayyana cewa a halin yanzu ba a bai wa shugabansu damar sanin cikakkun bayanai kan sabon tsarin da gwamnatin ke shirin yi ba. Don haka, suka buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su tuntuɓi shugabancin ƙungiyar, musamman Alhaji Sani Maisalati, domin tabbatar da sahihancin shirin da kuma kauce wa sake faruwar abin da ya faru a baya.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura da Mamallakansu a Jihar Kano, Alhaji Sani Abdul Mudallib Maisalati, mai unguwar Kofar Na’isa, ya bayyana cewa shirin sanya traka ba sabon abu ba ne a jihar Kano, domin an taɓa kawo irin wannan tsari har sau biyu a baya ta hannun wasu kamfanoni, amma duk an dakatar da su kafin kammalawa.

Ya ce yana kallon sake kawo wannan shiri karo na uku a matsayin abin da ka iya jefa al’umma cikin ruɗami, musamman idan ba a zo da cikakkiyar manufa da gaskiya ba.

A cewarsa, a duk lokacin da aka fara tsarin da kyakkyawar niyya, sai a yi nisa daga baya a ce an dakatar da shi, lamarin da ke jefa jama’a cikin asara.

Maisalati ya jaddada cewa a lokutan baya an karɓi kuɗaɗe daga mambobin ƙungiyar bisa niyyar sanya traka domin kare lafiyarsu, dukiyoyinsu da kuma inganta tsaro. Amma daga bisani aka dakatar da shirin ba tare da an mayar da kuɗaɗen da aka karɓa ba, abin da ya ce bai dace ba.

Ya bayyana cewa tsarin da aka bi a baya ya haɗa da cikakken rajista, inda ake buƙatar bayar da suna, adireshi, unguwa, lambar mota, sunan mai mota, lambar waya, adireshinsa da takardun shaidar mota. Bayan kammala duk waɗannan sharuɗɗa, sai a buga lamba a jikin mota ko adaidai-sahu, daga nan a ce za a sanya traka, amma daga ƙarshe aka dakatar da shirin.

Ya ce mambobin ƙungiyar ba sa jin daɗin irin wannan tsari.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar na wakiltar al’umma ne, don haka bai dace a riƙa kallon mambobinta kamar ana haɗa kai da su domin a yaudare su ko a cuce su ba.

Ya ce tun da ana shirin aiwatar da tsarin traka karo na uku, wajibi ne gwamnati ta bi hanyoyi masu gaskiya da bayyani wajen wayar da kan mambobin ƙungiyar, domin kawar da shakku da fargabar da ke zuciyarsu sakamakon abin da ya faru a baya.

A ƙarshe, mambobin ƙungiyar masu tuka motocin kurkura da mamallakansu sun bukaci gwamnatin jihar Kano da ta duba batun kuɗaɗen da suka biya a baya har sau biyu domin tsarin traka da aka dakatar, ba tare da an mayar musu da kuɗaɗen ba.

Sun yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakai na adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa duk wani sabon tsari da za a aiwatar zai kasance a bayyane.

Sun kuma jaddada cewa a kowane lokaci suna biyayya da goyon bayan duk wani tsari da zai inganta tsaro da cigaban jihar Kano, muddin aka aiwatar da shi cikin adalci da gaskiya.

  • Related Posts

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Lawan Ɓatagarawa, ya jaddada muhimmancin haɗa kai tsakanin gwamnati da kowane ɓangare na al’umma domin magance matsalar tsaro a ƙasar nan. Ɓatagarawa…

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ƙungiyar KAPAG da ke ƙarƙashin jagorancin Hajiya Balaraba Ibrahim ta kai ziyara ga shugaban ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano, Hon. Sekure, a sakatariyar ƙaramar hukumar,…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta