Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Wata mata mai suna Malama A’isha Abubakar da ta haifi ‘ya’ya huɗu a jihar Kano ta roƙi Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya kawo mata ɗauki sakamakon matsanancin halin da take ciki na rashin abin shayar da jariranta.
Malama A’isha, wadda ta haifi ‘yan-huɗu – maza biyu da mata biyu, ta bayyana cewa har zuwa yanzu ba ta samu tallafin da Sakataren Gwamnatin jihar Kano ya yi alƙawarin za a ba su ba, tun bayan da Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya jagoranci ganin su da gwamnan.
Jariran, waɗanda aka sanya wa suna Fatima, Halima, Bilal da Abubakar, na cikin halin buƙata sakamakon rashin wadatar rayuwa, inda maigidansu ke fama da ƙarancin ƙarfi.
Ta ce halin da suke ciki ya tilasta wa mijinta har sayar da gidan da suke zaune, domin samun kuɗin sayen madarar jariran.
Uwar ‘yan-huɗun ta ƙara da cewa, a cikin watanni huɗu kacal, jariran na shan madarar da kuɗinta ke kai wa fiye da miliyan Naira, lamarin da ya fi ƙarfinsu ɗauka.
Saboda haka, ta yi kira ga Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a matsayinsa na shugaba mai tausayi, da ya duba halin da suke ciki tare da kawo musu agaji.
Haka zalika, ta nemi taimako daga Sarkin Kano, da kuma attajirai masu taimakon marasa ƙarfi, ciki har da Alhaji Aliko Ɗangote da Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabi’u, domin ceton rayuwar jariran.
A nata ɓangaren, wata Unguwar Zoma da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa a wasu jihohin ƙasar nan, gwamnati kan ɗauki nauyin kulawa ta musamman ga irin waɗannan jarirai, tun daga haihuwa har zuwa lokacin da suka girma, duba da cewa haihuwar ‘yan-huɗu ba ta yawaita faruwa ba.






