Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Domin cigaba da ƙarfafa danƙon zumunci, zuriyar Goronduma sun gudanar da taron haɗin kai da suka assasa tun shekaru da dama da suka gabata.
A bana ma an gudanar da taron ne a ranar Lahadi a babban ɗakin taro na gidan Mumbayya, inda taron ya samu halartar ’ya’yan zuriyar da dama daga sassa daban-daban.
Da yake zantawa da ’yan jarida, ɗaya daga cikin ’ya’yan zuriyar Goronduma, Alhaji Habibu Umar Goronduma, shugaban kamfanin Burodin Goronduma, ya bayyana cewa taron na da matuƙar muhimmanci domin haɗa kan ’yan’uwa da abokan arziƙi, tare da sabunta zumunci, murna da fahimtar juna.
Ya ce an shafe shekaru ana shirya wannan taro, tun daga lokacin da manya suka assasa shi, har zuwa yanzu da ƙananan ’yan’uwa suka karɓa suka ci gaba da raya shi.
Ya ƙara da cewa tun farko an fara gudanar da taron ne a gidan Farfesa Ali da ke Kan Tudu, kuma da yardar Allah taron ya cigaba da bunƙasa daga shekara zuwa shekara.
Alhaji Habibu Umar ya yi nuni da cewa tasirin taron ya bayyana ƙwarai, domin a baya akwai ’yan’uwa da dama da ba su san juna ba. Sai dai taron ya taimaka wajen gano juna, har ma da fahimtar cewa wasu mutanen da ake mu’amala da su a kasuwa ko makaranta ’yan’uwa ne na jini, wanda hakan ke ƙara kusanci da haɗin kai a tsakaninsu.
Ya bayyana cewa a yanzu ’yan’uwa sun ƙara fahimtar juna, suna taimakekeniya, tare da ƙarfafa auratayya a tsakanin zuriyar.
Ya ce hatta shi kansa ya yi ƙarin aure daga cikin zuriyar Goronduma, abin da ke ƙara tabbatar da muhimmancin zumunci.
Ya jaddada cewa kiyaye zumunci wajibi ne, umurni ne daga Allah da Manzonsa (SAW), kuma mai yanke zumunci yana fuskantar mummunan sakamako.
Alhaji Habibu Umar Goronduma ya ce ba su da tabbacin adadin yawan zuriyar Goronduma, sai dai suna daga cikin waɗanda ke bin umurnin Manzon Allah (SAW) na yin aure da hayayyafa, domin yin alfahari da al’umma a ranar Alƙiyama.
Ya ce dangin Goronduma suna da yawan gaske, kuma a gidansu kaɗai sun kai mutum 36.
Ya ƙara da cewa sun taso ne cikin kyakkyawar tarbiyya daga iyaye da kakanni, abin da ya taimaka musu wajen gudanar da harkokin kasuwanci da taimakon al’umma.
Ya bayyana cewa kamfanin Burodin Goronduma da sauran harkokinsu na samar da ayyukan yi ga ɗimbin mutane, musamman matasa, inda adadin ma’aikatan ke kaiwa fiye da mutum dubu ɗaya a ƙiyasin sa.
A cewarsa, abin da ke ƙara bunƙasa kamfanin Goronduma shi ne roƙo da gaskiya, samar da ingantattun kayayyaki, da kuma dogaro ga Allah wajen neman albarka.
Ya ce idan Allah Ya sanya albarka a cikin abu, babu abin mamaki a bunƙasarsa, domin babu wata dabara da ta fi yardar Ubangiji.






