Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban Jami’ar Sufuri ta ƙasa da ke Daura a Jihar Katsina, Farfesa Umar Adam Katsayal, ya bayyana cewa an sami gagarumin cigaba a harkar jirgin sama a ƙasar nan in aka yi duba da shekaru 100 da suka gabata da soma saukar jirgin sama na farko a Kano.
Ya bayyana haka ne a taron bikin cika shekara 100 da fara saukar jirgin sama na farko a Kano da aka gudanar a harabar filin saukar jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Ya yi nuni da cewa in aka yi duba da shekarun da suka biyo baya za a ga yanzu tashoshin sauka da tashin jirage sama suna nan da yawa a faɗin kasar nan, babu wata jiha ma da babu ko da ƙarami ne na ƙasa da ƙasa ma suna da yawa, ga kuma jiragen kasuwanci da na ɗaiɗaikun mutane da yawa. Haka kuma, akwai kamfanonin kula sufurin jirage suna da yawa.
Ya ce dangantakar Jami’ar Sufuri ta ƙasa ta Daura da yake jagoranta da taron gagaruma ce, domin Jami’ar Sufurin ita ce ta farko ba kawai a ƙasar nan ba, har ma da yammacin Afirka gaba ɗaya.
Ya ce Jami’ar an yi ta ne domin ta samar da ma’aikata na kamfanin jiragen sama da tashoshin jirage suke buƙata da duk wani ɓangaren sufuri, ban da jiragen sama kaɗai ba har na ƙasa da mota da na jiragen ruwa, ita Jami’ar aikinta ta bayar da gudunmawa na ilimin da ake buƙata a waɗannan ɓangarori.
Hon. Farfesa Umar Adam Katsayal ya ce yanzu ba ƙaramin matsayi Jam’i’ar Sufurin take da shi ba a ƙasar nan, ita ce ta farko a Afirka baki ɗaya da ta yi nisa a karatu, domin har ta ɗauki ɗalibai kashi na farko da kashi na biyu da kuma kashi na uku. Nan da shekara biyu za ta soma yaye ɗaliban da za su yi ayyuka a tashoshin jiragen sama da na ruwa da ɓangarori daban-daban na sufuri.






