Akwai Buƙatar Gwamnati Ta Ƙara Himma Don Kawar Da Gurɓatattun Magaguna A Ƙasar Nan -Pharmacy Halliru Binji

Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar masu harhada magunguna na ƙasa, kuma shugaban ƙungiyar Community Permacy na jihar Sakkwato, Pharmacy Ibrahim Halliru Binji ya bayyana taron da ake na ƙungiyar masu harhaɗa magunguna na ƙasa PSN karo na 98 a jihar Kano da cewa komai na tafiya yadda ya kamata a taron.

Ya bayyana hakan ne da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin taron ƙungiyar ta masu haɗa magunguna da ke gudana a jihar ko Kano ya ce su a jihar su ta Sakkwato, ƙungiyar tana samun cigaba sosai da haɗin kai yanzu haka ma su 40 suka zo taron na ƙasa daga Sakkwato daga cikinsu sama da 100.

Da ya juya kan lamarin gurɓatattun magaguna da ake samu a ƙasar nan ya ce abu ne mara kyau mara daɗi, kuma ya san gwamnati tana mutuƙar ƙoƙari domin kawar da lamarin, amma dai yana da kyau ta ƙara himma sosai domin akwai iyakoki da ake shigowa da su ta ciki ta hanyar da ba ta dace ba.

Pharmacy Ibrahim Halliru Binji ya ce, akwai mahalarta taron da suka kai kusan 2,500 da suka zo daga Sakkwato, kuma jihar Kano ta karɓi baƙuncinsu masu halartar taron da karramawa, don haka ya yi kira a kan ƙarin samun haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙungiyar a ƙasa baki ɗaya domin cimma nasara samar da magunguna ingantattu.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo