Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hukumar Tsaron Al’umma ta Ƙasa (Civil Defence) ta kafa wani kwamiti domin bincike kan zargin kisan wani matashi da ke taimaka mata a ofishinta na ƙaramar hukumar Fagge, Kano, wanda ake zargin wasu jami’anta sun yi sanadiyyar rasuwarsa.
Lamarin ya janyo fusatar al’umma, inda wasu matasa suka yi yunƙurin far wa ofishin Hukumar a Fagge, bisa zargin cewa an yi wa matashin duka har ya mutu a lokacin da ake tuhumarsa da aikata sata.
Wata majiya ta shaida cewa matashin mai suna Usman Abdullahi, wanda aka fi sani da Khalifa, ɗan unguwar Ɗandali a ƙwaryar Fagge, mutum ne da jami’an Hukumar suka amince da shi sosai, yana aiki tare da su a matsayin jami’in sa-kai. An zarge shi da satar kuɗi har naira miliyan ɗaya (₦1,000,000) da ake tarawa a ofishin Hukumar, da kuma ɓatar wani babur, lamarin da ya sa ya tsere.
Majiyar ta ce jami’an sun bazama neman sa, inda daga bisani suka kama shi a unguwar Sabon Gari.
’Yan’uwan mamacin sun zargi jami’an da yi masa mummunan duka da azabtarwa a cikin ofishin hukumar, ciki har da amfani da makamai masu kaifi, abin da suka ce ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Ko da yake wata majiya ta bayyana cewa an kai shi asibiti bayan da aka lura da ya galabaita, amma an tabbatar musu cewa ba zai rayu ba, daga nan aka dawo da shi ofishin Hukumar inda daga bisani ya rasu.
Bayan rasuwarsa, jami’an sun kai gawar Khalifa gidansu da ke Dandali, amma ’yan uwansa suka ƙi karɓa, suka mayar da gawar zuwa ofishin Civil Defence na Fagge, suna neman a bi musu hakkinsu bisa tanadin doka.
Wani ɗan’uwan mamacin ya ce, ko da matashin ya aikata laifi, bai dace jami’an su ɗauki doka da hannunsu ba, maimakon su miƙa shi gaban kotu.
Ya ce irin azabtarwar da aka yi masa ce ta janyo mutuwarsa, shi ya sa suka mayar da gawar ofishin Hukumar domin a samu adalci.
Fushin jama’a kan lamarin ya haifar da kone-konen tayoyi da yunƙurin far wa ofishin hukumar, sai dai gaggawar zuwan jami’an tsaro da kawo ɗauki, tare da amfani da hayaƙi mai sa hawaye, ya dakatar da tashin hankalin.
A halin da ake ciki, ana kuma zargin cewa Hukumar na ɗaukar wasu mutane marasa cancanta a matsayin jami’an sa-kai, tare da zargin karɓar makudan kuɗaɗe ba tare da cikakken tantancewa ba, lamarin da wasu ke cewa na janyo shigar bata-gari cikin harkokin tsaro.
Da yake tabbatar da kafa kwamitin bincike, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Hukumar tsaron al’umma ta ƙasa a jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙon murya da ya aikawa manema labarai a ranar Alhamis, biyo bayan zargin da ake yi wa jami’an ofishin Fagge da hannu a rasuwar matashin a ranar Laraba, 8 ga Janairu, 2026.
Mai magana da yawun rundunar ya ce shugaban Hukumar ya kafa kwamitin ne domin gudanar da cikakken bincike, tare da tabbatar da adalci.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai yi aiki tare da rundunar ’yan sandan jihar Kano, domin zurfafa bincike da ɗaukar matakin da ya dace kan lamarin.






