Gwamnonin Arewa Sun Kafa Asusun Tallafa Wa Tsaro, Kowace Jiha Za Ta Riƙa Ba Da Biliyan 1 Duk Wata

Daga Khalid Idris Doya

A ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin Arewa na yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi yankin, gwamnonin sun amince da samar da Asusun Gidauniyar Tsaro na yanki da suka tsara domin samar da wadatattun kuɗaɗe don ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin yankin Arewa.

Sun cimma wannan matsayar ne a yayin zaman haɗin guiwa na musamman tsakanin ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewan (NSGF) da Majalisar Sarakunan Arewa, wanda ya gudana a Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna ranar Litinin.

Shugaban NSGF kuma Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya shi ne ya jagoranci zaman, wanda aka cimma matsayar cewa kowace jiha daga cikin jihohi 19 da suke faɗin Arewa za su riƙa bayar da gudunmawar Naira biliyan ɗaya duk wata, kuma za a riƙa cirewa ne kai tsaye bisa tsarin da dukkanin masu ruwa da tsaki suka aminta.

Bayan cire kuɗin kai tsaye zai shiga asusun gidauniyar tsaron da aka samar domin yaƙi da matsalar tsaro ciki har da yaƙi da garkuwa da mutane.

Gwamnoni da sarakunan sun nuna cewa wannan matakin ya kamata a ɗauke shi tsawon lokaci domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunƙarar matsalar tsaro da ta addabi yankin tsawon shekaru.

A jawabin bayan taro wanda shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar ya ce, asusun gidauniyar kai tsaye zai tafi ne wajen inganta ayyukan hukumomin tsaro, inganta samar da bayanai na sirri, tallafa wa amfani da fasaha a ɓangaren aikin tsaro, da kuma kyautata tsarin kai ɗaukin gaggawa ga al’ummomin da ke cikin buƙatar kai ɗaukin jami’an tsaro a yayin da suke cikin barazana ta tsaro.

Sanarwar bayan taron wanda kakakin Gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ta ce, ƙungiyar ta miƙa jajenta ga mutane da gwamnatocin jihohin Kebbi, Kwara, Kogi, Neja, Sokoto, Jigawa, da Kano a bisa garkuwa da mutane da aka samu rahoton aukuwar su a cikin jihohin kwanakin baya, tare da jajanta wa waɗanda harin ‘yan ta’addan Boko Haram na baya-bayan nan ya shafa a jihohin Borno da Yobe.

Gwamnonin sun jinjina wa yunƙurin gaggawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka wanda hakan ya kai ga samun nasarar ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da su, tare da azama da yake ƙara sanyawa wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.

A yayin da suke jaddada matsayinsu da suka jima a kai, gwamnonin sun tabbatar da cikakken goyon bayansu ga kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, inda suka buƙaci ‘yan majalisar tarayya da na jihohi daga yankin da su hanzarta aiwatar da duk wani da ake nema domin ganin an sami nasarar wannan batun.

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda haƙo ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba ke ƙara ta’azzara wajen haifar da rashin tsaro, tare da yanke shawarar bai wa shugaba Tinubu shawarar cewa Ministan Ma’adinai ya dakatar da duk wani aikin haƙar ma’adinai na tsawon watanni shida. Hakan zai ba da damar gudanar da cikakken bincike da sabunta lasisin haƙar ma’adinai tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi.

Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya sun amince da muhimmancin haɗin kai, kuma ɗaukar maida hankali kan nauyin da ya rataya a wuyansu wajen tunƙarar ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

Sun yi alƙawarin ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, majalisar sarauta da al’umma domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa.

  • Related Posts

    Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar…

    Karamci da Mutumtaƙa: Dubban Jama’a Sun Cika Garin Kwankwaso a Ɗaurin Auren ’Ya’yan Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso

    Daga: Ibrahim Muhammad, Kano Garin Kwankwaso da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano ya cika maƙil da dubban jama’a daga sassa daban-daban na jihar da ma wajenta, yayin da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    An Kammala Baje Kolin Kano Na 46 Cikin Nasara

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Gwamnatin Zamfara Ta Bunƙasa Harkar Kasuwanci Da Zuba Jari Da Haƙo Ma’adanai -Tafidan Maradun

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe

    Kasuwar Galadima Ta Fara Aikin Sabunta Gadar Shiga Kasuwa Da Ta Rushe