Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban ƙaramar hukumar Ƙaraye Hon. Haruna Safiyanu ya bayyana cewa su a tsarinsu na Kwankwasiyya tamkar iyali ɗaya suke tafiya duk abin da ya samu ɗaya a cikinsu ya same su ne gaba ɗaya shi ya sa suka taru domin taya mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan siyasa Hon. Sanusi Sirajo Kwankwaso don taya shi murna na ɗaurin auren ‘ya’yansa a garin Kwankwaso.
Ya ce a matsayinsa na ɗan siyasa ɗan Kwankwasiyya idan aka yi duba da yadda gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ke tafiyar da ayyukansa a birni da karkara da yadda ya sahale musu suke yi a karkara, don haka zaɓen 2027 suna cikin nasara, da yardar Allah gwamnati za ta ɗore saboda irin ayyuka da take na alheri.
Hon. Haruna Safiyanu ya bayyana cewa, “Yadda Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kasafin kuɗi na bana kuma har ya yi alƙawarin bunƙasa karkara mun san shi da faɗa da cikawa, da yardar Allah yadda ya mayar da birni, haka zai mayar da karkara da izinin Allah,” in ji shi.
Ya ce a matsayinsa na shugaban ƙaramar hukumar Ƙaraye a shekara ɗaya da zaɓar su da aka yi suna jin daɗin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sahale wa shugabannin ƙananan hukumomi suke ta gudanar da ayyuka daban-daban na cigaban al’umma ya fi aikin da waɗanda suka shekara takwas suka tafi ba su yi kamar su ba. “Wannan babban abin alfahari ne ƙwarai da gaske a wannan gwamnati tamu mai albarka,” ya jaddada.
Shugaban na ƙaramar hukumar Ƙaraye Hon. Haruna Safiyanu ya ce babu wata mazaɓa a yankin da ba su je sun gudanar da ayyuka ba, kama daga gyara da gina sabbin makarantu da gina hanyoyi da gadoji, kuma a sabon kasafi da aka yi bana za a ga ayyuka da za a yi tamkar ba a yi komai ba ne a wannan shekarar.
Hon. Haruna Safiyanu Ƙaraye ya ce a harkar gudanar da aikinsu na mulki don cigaban ƙaramar hukumar Ƙaraye kansu a haɗe yake tun daga kan shugabanin jam’iyyar NNPP na yankin da ma’aikata da kansilolinsu zaɓaɓɓu da na naɗi suna tare da su ana tafiyar da mulki yadda ya kamata suna bunƙasa cigaban ƙaramar hukumar.






