Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Wasu daga cikin mahajjatan da suka sauke farali a shekarar 2023 daga jihar Kano sun yi ƙorafin cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ba ta mayar musu da Dala 100 da aka cire daga guzurinsu ba, duk kuwa da cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta riga ta dawo da kuɗaɗen ga mahajjatan.
Mahajjatan sun bayyana cewa tun a lokacin shirin tafiya aikin Hajji, an cire musu Dala 100 daga cikin Dala 700, inda aka ba su Dala 600, bisa dalilin kewaye da aka ce za a yi wa mahajjata sakamakon rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan. Daga bisani kuma aka sanar da cewa za a dawo musu da kuɗin da aka cire.
Sun ce daga baya Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta umarci duk mahajjatan da abin ya shafa da su je su karɓi Dala 61,000, wanda shi ne daidai da kimar musayar Dala 100 a shekarar 2023. Sai dai, yayin da aka biya wasu daga cikinsu, har yanzu akwai da dama da ba a biya su ba.
Mahajjatan sun ƙara da cewa duk ƙoƙarin da suka yi na neman bayanin inda kuɗaɗen nasu suka tsaya daga wajen Hukumar bai haifar musu da sakamako ba. Hakan ne ya sa yanzu suke kira ga gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf da kuma Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Lamin Ɗan Baffa, da su shiga tsakani domin bincike da kuma mayar musu da haƙƙinsu.
Sun bayyana cewa sun yi shiru na tsawon lokaci ne da fatan cewa daga bisani za a warware matsalar, sai dai ganin yadda lokaci ke wucewa ba tare da wani mataki ba, ya sa suka yanke shawarar bayyana damuwarsu a bainar jama’a.
Mahajjatan sun ce a shirye suke su bayar da dukkan haɗin kai da ake buƙata domin gudanar da sahihin bincike, domin gano inda kuɗaɗen suka maƙale, suna mai gargaɗin cewa cigaba da yin watsi da lamarin na iya janyo zargin almundahana a tafiyar da harkokin Hukumar.






