Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,000 Da Suka Halarci Taron Baje Koli A Kano -Dakta Rahila Aliyu Muktar

Daga Ibrahim Muhammad

Shugabar hukumar taimakekeniyar kula da lafiya ta jihar Kano, Dakta Rahila Aliyu Muktar ta bayyana godiya ga Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa sahale musu da ya yi suka halarci taron baje kolin na 46 domin yi wa al’umma hidima ta duba lafiyarsu kyauta da ya haɗa da duba ido da ba da labarai na ƙara gani da duba haƙora wanda aƙalla sun duba mutum sama da 2000.

Ta ƙara da cewa a filin baje kolin sun bayar da dama ga al’ummar jihar Kano da suke karɓar gudunmawa a ƙarƙashin kulawar hukumar su kawo ƙorafe-ƙorafe da suke da shi a yayin da suka je a kula da lafiyar su a asibitocin jihar Kano, kuma sun sami haske kan hakan domin ma’aikata da yawa musamman malamai na makaranta sun kawo ƙorafe-ƙorafe sun rubuta za su ɗauki mataki a kai.

Dakta Rahila Aliyu Muktar ta ce sun gode wa Allah da suka samu shaidar yabo bisa gudunmawa da suka bayar har aka karrama su a ƙarshen baje kolin wannan ya nuna musu su ƙara yin ɗamara da haɓɓasa ne a aikin da suke na kula da inganta lafiyar al’umma.

Ta yi nuni da cewa su kullum ƙofofinsu a buɗe suke domin so suke a kawo musu ƙorafi a kan duk asibitin da suke hulda da shi in ya gaza, saboda yarjejeniya suka yi da su na aiki na cewa za su ba da magunguna masu inganci, kuma a tsarin hukumar taimakekeniyar kula da lafiya ta jihar Kano an ce a sai magunguna daga DMCSA, kuma ita kaɗai aka amince a saya a wajenta domin hukumace mai zaman kanta da take da shugaba jajirtacce duk magani da ya kawo mai inganci ne.

Ta ce duk magunguna yadda suka yi yarjejeniya da asibitoci shi ne su sai magani a DMCSA, kuma in sun saya a nan tabbas mai kyau ne da inganci, amma tabbas akwai waɗanda suke saba wannan yarjejeniya in suka bincika suka same su suna da kotun tafi da gidanka da take hukuntasu shi ya sa suke cewa al’umma in sun je an saba musu, akwai lambobi da za su kira ko su zo hukumar su kawo ƙorafi za su ɗauki mataki a kai don ba sa so mutum ya je a kula da lafiyarsa a ce an zalunce shi Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce bai yarda da haka ba.

  • Related Posts

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Daga Ibrahim Muhammad Ƙungiyar masu tuƙa motocin ƙurƙura da mamallakansu a jihar Kano, ta ja hankalin Gwamnati da ta yi taka-tsantsan wajen shirin dawo da tsarin sanya traka a ababen…

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Lawan Ɓatagarawa, ya jaddada muhimmancin haɗa kai tsakanin gwamnati da kowane ɓangare na al’umma domin magance matsalar tsaro a ƙasar nan. Ɓatagarawa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta