Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana yin karatu da cewa muhimmin abu ne mai kyau da yin sa ne ya sa suka samu dama suke aiki a garuruwa daban-daban, kuma duk inda suke suna cigaba da alfahari da daga inda suke don yin hakan abu ne mai kyau da ƙara masu daraja a cikin jama’ar da suke.
Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Saminu Madaci ne ya bayyana hakan da yake hira da ‘yan jarida bayan karrama shi da ƙungiyar al’ummar Rano, Kibiya da Bunkure suka yi a garin Rano a yayin taron karrama ‘yan asalin yankin.
Ya ce kyakkyawan hali abu ne mai kyau da matasa na ƙasa masu tasowa za su koya abu ne mai muhimmanci kowa ya yi ƙoƙarin neman ilimi ko da za ta kama iyaye ko da gona ne za su sayar don yara su yi karatun, to cin riba ce gare ka da kuma a dogara sai an yi aiki samun ilimin kaɗai zai amfani wanda ya yi da al’umma ya kuma ƙara maka wayewa.
ACP Saminu Madaci ya ƙara da cewa, “Ba lallai ne ka taso a garinka ka yi karatu ka zauna dindindin ba. Za a iya samun yanayi ko na aiki da za ka zaga ka shiga cikin al’umma daban-daban ka ga al’adu da zamantakewa masu kyau da za ka koya su ma su koyi naka.”
Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan Saminu Madaci ya ce sun ji daɗi da al’ummarsu ta Rano suka karrama su su a matsayinsu na manyan jami’an ‘yan sanda da aka tattaro ‘yan asalin yankin da sauran mutane daban-daban aka karrama.
Ya yi nuni da cewa Karramawar za ta ƙara musu ƙwarin gwiwa da ƙaimi wajen cigaba da taimaka wa yankinsu, kuma hakan ya zama darasi ga wasu su koya.
Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Saminu Madaci ya ce a baya kafin wannan an yi masa irin wannan karramawar, yanzu kuma da ya sake samun ƙarin matsayi na ACP an karrama shi, kuma mutane da yawa sun taru sosai duk da cewa yana zaune ne a Abuja sauran waɗanda aka karrama su tare jami’an ‘yan sanda suna ayyuka ne a wurare daban-daban a ƙasar nan sun ji daɗin haɗa su da aka yi da karramawa da RAƘIBU ta yi musu.






